An zargi Trump da wariyar launin fata

Rashida Tlaib (tsakiya) da Alexandria Ocasio-Cortez (hagu) da kuma Ayanna Pressley (dama) Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rashida Tlaib (a tsakiya), wadda ta mayar da martani da kiran Trump, shugaban kasa maras bin doka wanda ya gaza kacokan, da Alexandria Ocasio-Cortez (a hagu), da kuma Ayanna Pressley (a dama)

An zargi Shugaban Amurka Donald Trump da nuna wariyar launin fata, bayan wasu sakonni da ya sanya a shafinsa na Twitter, wadanda a ciki yake sukar wasu mata 'yan majalisar wakilan Amurkar.

Duk da cewa bai ambaci sunayen matan ba, amma ya ce sun fito ne daga kasashen da gwamnatocinsu kamar yadda ya ce, tsabagen bala'i ne; ya rubuta hakan ne kuwa duk da cewa an haife yawancin wadannan mata 'yan majalisa a Amurkar.

Mista Trump bai tsaya a nan ba, har ma ya nemi da su koma gida wato kasashensu na asali.

Mata hudu 'yan majalisar wakilan Amurkar da ake ganin shugaban kasar ya yi wa wannan gugar zana , dukkaninsu an zabe su a lokacin zaben rabin wa'adi na shekarar da ta wuce.

Kuma akidarsu ta siyasa ta ra'ayin kawo sauyi, ko gaba-dai gaba-dai ta sa sun yi ta samun sabani da shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi , musamman ma a kan manufa ko batun shige da fice.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An zargi Shugaba Trump da wariyar launin fata da kuma fifita farar fata

Daya daga cikin matan, Ilhan Omar, an haife ta ne a Somalia, amma kuma tun tana karama aka je da ita Amurka.

Sauran ukun kuwa, Rashida Tlaib 'yar Falasdinu ce, sai Ayanna Pressley, 'yar asalin Afirka, sai kuma Alexandria Ocasio-Cortez, tsatson Spaniya da sirkin Afirka.

Dukkanin wadannan matan guda uku daga cikin hudun, an haife su ne a Amurka., hasali ma ita Alexandria, tazarar mil 12 ne tsakanin mahaifar Donald Trump da inda aka haife ta, a New York.

A jerin sakonnin Tweeter, da ya rubuta Shugaba Trump ya bayyana gwamnatoci da kasashen da matan na asali, wadanda suka fi cin hanci da rashawa, wadanda kuma ba su dace ba a duk fadin duniya.

Sannan kuma ya zargi matan da fita karara suna daga murya da kwakwazo suna gaya wa 'yan Amurka wai yadda ya kamata su tafiyar da gwamnatinsu.

Ya kara da cewa; ''Me zai hana su koma, su taimaka a gyara can inda suka samo asali inda abubuwa suka tabarbare, miyagun laifuka suka mamaye, suka samu gindin zama.

Dukkanin matan hudu dai sun mayar wa da Mista Trump din martani, su ma ta Tweeter, inda Rashida Tlaib ta kira Trump, shugaban kasa maras bin doka wanda shugabancinsa kacokan asara ne.

Shugabar majalisar wakilan Amurkar, Nancy Pelosi, ta yi Allah-wadarai da kalaman na Mista Trump, tana mai bayyana su a matsayin na kyamar 'yan wasu kasashe.