Angela Merkel: Me ke sa shugabar Jamus yawan karkarwa?

Angela Merkel Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Duk fitowar da ta yi, mutane sun zuba ido domin ko za su ga wata alamar rashin lafiya tare da ita

Angela Merkel dai za ta cika shekara 65 a ranar Laraba, amma duk da cewar mutane suna ta wasi-wasi a kan lafiyarta , ta zabi ta ci gaba da aikinta har sai karshen wa'adinta da zai kare a 2021.

An sha ganin ta tana karkarwa a wasu tarukan da aka yi kuma hakan ya janyo ce-ce ku-ce a kan lafiyarta tsakanin al'ummar Jamus.

A yayin da ta kusan kai shekarun ritaya a Jamus, mutane sun sa mata ido don gano me ke faruwa da ita.

Kanun labaran wasu jaridu sun kasance tamkar tambaya kan ko tana da lafiyar da za ta ci gaba da aiki.

Masana harkokin lafiya dai sun amince da su gudanar da bincike daga nesa kan wani shirin talabijin game da lafiyar tata.

Shugabar gwamnatin Jamus din ta yi bikin cikarta shekara 60 a duniya ta hanyar halartar wani taro kan duniya.

Lokacin da ta cika 50 kuwa, an mayar da hankali ne kan tattaunawa tare da wani masanin kimmiyar kwakwalwa.

Mutane da dama dai ba haka za su nuna jin dadinsu ba, amma fa wadannan taruruka ne da aka kururuta. A ranar zagayowar ranar haihuwarta ta wannan shekarar, ana ganin cewa za ta zabi zama a gida kawai.

Yadda karkarwar ta fara

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugabar jam'iyyar Jamus ta Christian Democratic Union (CDU) Annegret Kramp- Karrenbauer da kuma shugabar gwamnatin Angela Merkel

Lokaci na farko da aka fara ganin tana karkarwar wata rana ce a watan Yuli, lokacin da ta gayyaci sabon shugaban Ukrain zuwa Berlin.

Ana tsaka da rera taken kasar, sai ta fara karkarwa mai tsanani. Bayan 'yan mintuna kadan sai ta dawo dai-dai ta ci gaba da taron ba tare da wata matsala ba.

Daga baya sai ta bayyana cewa yanayi mai zafi ne da rashin shan ruwan da ta yi ya janyo mata karkarwar.

Kwana tara bayan nan, sai aka kara ganin lamarin ya same ta a wani taron da ta yi da shugaban Jamus.

A cikin makon da ya gabata ma, mutane sun gan ta tana karkarwa lokacin da ta ke gaisawa da Fraiministan Finland wanda ta gayyata zuwa Berlin --- kuma lamarin ya same ta ne dai-dai lokacin da ake rera taken kasar tata.

A cewar wani mai magana da yawun gwamnatin kasar, ''abin da ya janyo karkarwarta karo na uku shi ne tsoron kar abin ya kara samunta ne, sai kwakwalwarta ta janyo mata wannan karkarwar''.

A rana ta gaba dai, domin ta kaucewa lamarin ya kar ya kara samun ta, a yayin da take gaisawa da Fraiministar Denmark sai suka zauna a lokacin da ake rera taken kasar maimakon su tsaya a tsaye. Hakan ya kara faruwa a ranar Talata da shugaban Moldova ya je kasar.

Misis Merkel ta jima tana jaddada cewa lafiyarta kalau kuma za ta iya aiwatar da aikin nata ba tare da matsala ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Merkel na karbar bakuncin shugabanni duk da halin da take ciki

'Yan siyasa sun sa ta a gaba

A ranar Litinin mai magana da yawunta ta gabatar da jawabi kan dalilin da Mrs Merkel ta bayyana kamar ba ta iya numfashi a wata ziyarar da ta kai zuwa birnin Paris.

Lamarin dai ya bai wa abokan hamayyarta na siyasa damar tofa albarkacin bakinsu.

Tsohon shugaban leken asiri Hans-Georg Maassen, wanda babban mai sukar Mrs Merkel ne wanda kuma aka tilasta masa barin aikinsa bayan da aka zarge shi da tunzura rikici.

Ya kuma wallafa a shafinsa na twitter cewa: ''Lafiyar shugabar gwamnati ba lamarin sirri ba ne a Jamus kuma muna da damar mu bukaci sanin ko shugabar gwamnati za ta iya ci gaba da aiwatar da aikinta ba tare da wata matsala ba.

Yawancin kafafen sada zumunta dai sun ce ya kamata a bar wa Mrs Merkel sirrin ta, a kuma daina daukarta a matsayin makaryaciya.

Yawancin masu zabe a Jamus dai sun amince da hakan. A cewar wani bincike, kashi 59 sun yarda cewa Mrs Merkel ba dole sai ta bayyana abin da ke damunta ba. Kashi 34 kuma sun musanta hakan.

Wa zai gaji Merkel?

Annegret Kramp-Karrenbauer wacce ke jagorantar CDU bayan wasu rikice-rikice, ita ce wadda Mrs Merkel take son ta gaje ta.

Wani lokaci ma ana ganin kamar Mrs Merkel ce kawai ke hana wani rikici.

Idan ta kasa ci gaba da rike mukaminta, a cewar kundin tsarin mulkin ba wanda zai gaje ta cikin gaggawa, har sai shugaban Jamus ya saka sabon shugaban gwamnati sannan sai majalisar dokokin kasar ta zabi sabo.

A yanzu dai, Mrs Merkel za ta ci gaba da aikinta mai tsauri kuma ba ta fasa gana wa da shugabanni ba.

Aiki zai ci gaba, amma kuma tsaurin aikin zai karu.

Labarai masu alaka