An gano masallacin da ya shekara 1,200 a Isra'ila

An ancient mosque found in the Israeli desert - Wani masallacin zamanin da da aka gano a tsakiyar hamadar Isra'illa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption The mosque was found in the Israeli Bedouin town of Rahat in the Negev desert - An gano masallacin ne a garin Rahat na kasar Isra'illa da ke hamadar Negev.

Masu hako kayan tarihi sun gano daya daga cikin masallatan da aka fara sani a duniya, wanda aka gina shekara 1200 da suka gabata a Hamadar Negev a Isra'ila.

An gano baraguzan masallacin ne a garin Larabawa Makiyaya na Rahat.

An dai gano wasu baraguzan masallacin wanda aka gina a karni na 7 ko 8 a garin Rahat.

Hukumar Adana Kayan Tarihi ta Isra'ila (IAA) ta ce an gano masallacin ne a lokacin da ake kokarin yin wasu gine-gine a filin da masallacin ya ke.

The ruins of a mosque found in Israel - Hoton masallacin kenan da aka gano a Isra'illa Hakkin mallakar hoto Israel's Antiquities Authority
Image caption An gano masallacin ne a yayin da ake kokarin yin wasu ayyukan gine-gine
Muslims pray at the site of an ancient mosque in Israel - Musulmai kenan lokacin da su ke sallah a masallacin na zamanin da a kasar Isra'illa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu musulmai kenan a lokacin da suke sallah a cikin zagayenn masallacin da aka gano

Shi ne masallaci na farko da ya shahara a zamanin da, kuma masallacin ya yi tashe ne a dai dai lokacin da masallatan da aka gano a Jerusalem da kuma Makkah suka yi tashe.

Daraktoci masu hako abubuwan da, Jon Seligman da kuma Shahar Zur sun ce gano masallacin da aka yi abin mamaki ne a duk fadin duniya.

Masu bincike sun kiyasta cewa masu sallah a masallacin manoman karkara ne.

A worker from Israel's Antiquities Authority at the site of an ancient mosque - Wani ma'aikacin Hukumar Isra'illa mai kulla da abubuwan da aka hako a wurin da aka gano masallacin na zamanin da. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shahar Tzur na hukumar na Hukumar Isra'ila mai kula da abubuwan da aka hako kenan ya ke bayar da bayyanai kan masallacin

Ginin dai ba shi da rufi kuma mai kusurwa hudu ne, sa'annan kuma an gina shi ne yadda ake gina masallatai, kuma alkiblarsa na kallon Makkah wato birni mafi tsarki ga musulmai.

''Fasalin ginin dai ya sa aka gano me ainihin amfanin ginin na daruruwan shekarun da suka gabata,'' a cewar Mr Seligman.

A worker from Israel's Antiquities Authority at the site of an ancient mosque - Wani ma'aikacin Hukumar Isra'illa mai kulla da abubuwan da aka hako a wurin da aka gano masallacin na zamanin da. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yasar Alamor na Hukumar Isra'ila mai kula da abubuwan da aka hako a lokacin da ya ke nuna wani dutsen da aka gano a cikin masallacin

Wannan masallacin dai shi ne daya daga cikin masallatan da aka gina a lokacin da aka fara aiwatar da addinin musulunci, a wurin da a yau ake kira Isra'ila, lokacin da Larabawa suka kwace yankin Byzantine a shekara ta 636 a cewar wani masanin tarihin adinnin Musulunci Gideon Avni.

''Gano masallacin da kuma kauyen da aka yi gagarumar karuwa ce ga binciken da ake yi kan tarihin kasar a dai-dai wannan lokacin da ake ci gaba da zaman dar-dar,'' a cewarsa.

Dukannin hotunan hakkin mallakarGetty da kuma Hukumar Isra'ila mai kula da abubuwan da aka hako ne.

Labarai masu alaka