Kalli hotunan yadda Amurkawa ke maganin tsananin zafi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yara na wasan wanka a wurin shakatawa na Domino Park, a New York

A yanzu Amurka na fuskantar yanayi mai tsananin zafi, inda ya kai lamba 38 a ma'aunin Selshiyas.

Lamarin ya fi tsanani a jihohin da ke yankin gabar gabas (East Coast) ta tekun kasar, inda jama'a a New York da Philadelphia da kuma Washington suke fama da dan-karen zafi.

Daman kusan wadannan jihohi sun fi Phoenix da Arizona da kuma Miami a Florida zafi.

An bukaci mutanen yankunan da abin ya shafa da su tabbatar suna shan wadataccen ruwa, sannan kada su fita waje idan ba ya zama dole ba, kuma su rika kula da mutane masu rauni, wadanda suka hada da marassa lafiya, da yara da kuma tsofaffi.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Mutane na kokarin sanyaya jikinsu ta duk wata hanya da za su iya, inda ake ganin mutane sun cika a tafkunan wanka na gwamnati da duk inda ake da ruwa da ke zuba.

Tafkin wanka na Astoria Pool da ke Queens, a New York City, ya cika da jama'a a ranar Asabar.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wannan yaron shi kuwa ya je wurin famfon da ke watsa ruwa ne na jika shukoki, yana jika jikinsa saboda maganin zafin, a kusa da Astoria Park.

Hakkin mallakar hoto AFP

Magajin garin birnin New York Bill de Blasio ya ayyana cewa birnin na cikin yanayi na tsananin zafi, kuma a karon farko cikin shekara 18 an soke gasar tseren keke da linkaya da kuma gudu ta birnin wadda a da za a fara ranar Lahadi.

Kusan mutane 4,000 ne aka sa ran za su shiga gasar, inda yawancinsu kan je daga wurare masu nisa domin halarta. Masu shirya gasar sun ce za a mayar wa da masu shiga kallon gasar cikakken kudin tikitinsu, wanda ya kai dala 399.

An samar da wuraren wanka ko jika jiki sama da 500 ga mazauna birnin New York City.

A Boston da ke Massachusetts, mutane manya da yara na ta tururuwa zuwa wuraren da ake da inda ruwa ke zuba domin sanyaya jikinsa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani dan yawon bude idanu ne nan ya kare kansa daga zafin rana da littafin jagora ko sanin gari na fadar White House.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ba mutane ne kadai suke cin moriyar ruwan sanyin ba. Su ma wadannan tsuntsayen biyu ba a bar su a baya ba, kamar yadda ake gani an dauki hotonsu suna wanka a lambun Rose Kennedy Greenway a Boston.

Hakkin mallakar hoto Reuters

A Philadelphia, an ga wani kare yana sanyaya jikinsa a wani wurin abin kashe gobara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka