Iran za ta kashe masu leken asirin Amurka

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
A ranar Alhamis ne Iran ta saki wani bidiyo na yadda ta kwace jirgin ruwan dakon mai da aka yi fasa kwaurinsa

Iran ta ce ta kama masu leken asirin Amurka 17 da suke wa CIA aiki, ta kuma yankewa wasu daga cikinsu hukuncin kisa.

Ma'aikatar leken asiri ta ce wadanda ake zargin sun yi ta karbar bayanai ne kan bangaren nukiliya da soji da kuma sauran bangarori.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da zarge-zargen Iran din, yana mai cewa "duk karya ne."

Iran da Tehran suna ta samun rashin jituwa kan shirin nukiliyar Iran kuma hankula na kara tashi.

A bara ne Mista Trump ya yi watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta kasa da kasa, kuma Amurka ta sake kakaba musu takunkuman tattalin arziki.

A makonnin da suka gabata, kasashen sun kusa tafka yaki a mashigar Tekun Fasha.

Da yake magana jim kadan bayan sanarwar ta Iran ya ce, Mista Trump ya ce: "Zai yi min matukar wahala na yi wata yarjejeniya da Iran."

Me muka sani a kan batun 'leken asirin'?

Iran ta ce an kama masu leken asirin wadanda ake zargin su da yi wa Hukumar Leken Asirin Amurka ta CIA aiki ne cikin wata 12 har zuwa wata Maris din wannan shekarar.

Dukkan mutum 17 din suna aiki ne a "muhimman wuraren kasar Iran" na soji da cibiyoyin nukiliya da kamfanoni masu zaman kansu, kamar yadda wani babban jami'in Iran ya shaida wa manema labarai.

Bai fadi ko mutum nawa aka yankewa hukuncin kisa ba ko lokacin da za a aiwatar da hukuncin.

An ruwaito Shugaban Ma'aikatar Leken Asirin Iran yana cewa: "An yanke wa wadannan 'yan leken asiri hukunci--wasu daga cikinsu hukuncin kisa saboda lafin 'fasadi a bayan kasa' (laifin da hukuncinsa kisa a dokokin shari'ar Musulunci na Iran",

A ranar Lahadi, Ministan Leken Asiri Mahmoud Alavi ya sanar da cewa za a nuna wani shiri na talbijin kan kama "masu leken asirin Amurkan" a gidan talbijin na Iran.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Me ya sa aka damu da Mashigar Ruwan Hormuz?

Ma'aikatar leken asirin ta Iran ta kuma saki wani faifan CD mai dauke da tallan fim din, inda aka kwaikwayi tarurrukan leken asiri da hirarraki da wasu jami'ai, ciki har da MIsta Alavi

Wasu daga cikin masu leken asirin sun fada tarkon neman visar da CIA ta dana wa wasu Iraniyawa da ke son zuwa Amurka in ji Mista Alavi, yana mai kara wa da: "An tuntubi wasu ne lokacin da suke neman visa, yayin da sauran kuwa dama suna da visa amma CIA ta matsa musu lamba su sabunta su."

Ya ce sauran kuwa an ja hankalinsu ne da kudi da ayyuka masu gwabi da kuma ayyukan kula da lafiya.

Kafar talbijin ta kasar Iran ta nuna wani shiri a kan matsalolin da ke cikin "hukumar CIA."

A watan da ya gabata, Iran ta ce ta tarwatsa kungiyar wasu mutane me alaka da CIA, amma ba a sani ba ko sanarwar ranar Litinin na da alaka da wannan lamarin.

Shin Iran na samun karfi ne ta ko yaya?

Sharhi daga Kasra Naji, BBC Fasha

Masu sa ido da dama a harkokin siyasar Iran na tababar sabon ikirarin Iran din.

A ranar Litinin ne ma'aikatar leken asirin Iran ta ce ta rusa kungiyar wasu mutane da ke da alaka da CIA a watan da ya gabata.

Amma wani abin rikitarwar shi ne ma'aikatar ta kara da cewa an kama mutum 17 din da ake zargi da leken asirin ne a bara.

Wasu sun yi amannar mutum 17 din jumullar yawan wadanda aka kama da zargin leken asiri ne a shekaru da dama. Dukkansu Iraniyawa ne.

A cewar wani daga gidan yarin Evin da ya yi kaurin suna, akwai mutane da dama a can da ake zarginsu da leken asiri daga kasashe daban-daban.

Amma dalilin da ya sa ma'aikatar leken asirin ta fitar da wannan labari a yanzu shi ne wata kila tana da abin yi sosai kan adawarta da bangaren leken asirin Sojojin Juyin Juya hali fiye da sabbin kamun.

Amma mako biyu da suka gabata gidan talbijin na Iran ya nuna kashi na karshe na shirin da ke yabawa bangaren leken asirin da kuma nuna gazawar Shugaba Hassan Rouhani kan magance leken asirin kasashen yamma.

Mene ne ya fara jawo rikicin?

Tashin hankali tsakanin Iran da Amurka da Birtaniya yana kara kamari, bayan da aka yi ta samun rigingimu a yanki mai muhimmanci da jiragen ruwa ke hada-hada a duniya, Mashigar Ruwan Hormuz:

  • A ranar Juma'a, Iran ta kwace wani jirgin ruwan dakon mai na Birtaniya a tekuna masu muhimmanci na duniya. A baya Iran ta sha gargadin cewa za ta mayar da martani bayan da Birtaniya ta kama jirgin ruwan dakon manta a gabar tekun Gibraltar a farkon watan nan
  • A makon da ya wuce Mista Trump ya ce rundunar sojin ruwan Amurka ta lalata jirgi marar matukin Iran bayan da ya ki janyewa, amma Iran ta musanta hakan
  • A watan da ya gabata, Iran ta harbo wani jirgi marar matuki mai sintiri a saman mashigin ruwan strait, tana zarginsa da keta sararin samaniyar Iran ba bisa ka'ida ba. Amma rundunar Sojin Amurka ta ce jirgin yana shawagi ne a sarrain tekunan duniya a lokacin, tana mai yin Allah-wadai da harin da Iran ta kai masa
  • Amurka ta kuma zargi Iran kan wasu hare-hare biyu da aka kai kan jiragen dakon mai a Mashigin Kogin Oman a watan Mayu da Yuni - zarge-zargen da Iran ta musanta
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani kyalle da aka yi rubutun nuna adawa da Amurka a wajen sallar Juma'a a Tehran

Tashin hankali tsakanin kasashen biyu ya ta'azzara tun da Amurka ta tsaurara takunkumai kan bangaren man fetur na Iran bayan da ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a 2015.

Labarai masu alaka