Isra'ila ta rushe gidajen Falasdinawa

Motar rusau ta Israila tana rushe gida a Wadi Hummus ranar 22 ga watan Yulin 2019. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kotun kolin Isra'illa ta ce an gina gidajen ba bisa ka'ida ba kuma suna kawo barazanar tsaro

Isra'illa ta fara rushe wasu gidajen Falasdinawa wadanda aka ce an gina ba bisa ka'ida ba kusa da iyakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Dakarun tsaron sun afka wa unguwar Sur Baher da ke gefen gabashin birnin Kudus domin rushe gidajen da ke da mazauna 17.

Mazaunan sun bayyana cewa hukumomin Falasdinu ne suka ba su takardun izinin gina gidajen kuma sun zargi Isra'illa da yunkurin kwace filin da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Amma kotun kolin ta Isra'ila ta yanke hukuncin cewa gidajen sun keta dokokin gine-gine.

Isra'ila ta kwace yankin na Gabar Yammacin Kogin Jordan a shekara ta 1967 a yayin yakin Gabas ta Tsakiya da aka yi kuma daga baya ta hade yankin da gabashin Kudus.

Karkashin dokokin kasa da kasa, dukkanin yankunan biyu an dauke su a matsayin yankunan da ke da mazauna, duk da cewar Isra'ila ta musanta hakan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mazauna gidajen sun bayyana cewa hukumomin Falasdinu ne suka ba su takardun izinin gina gidajen

Wasu 'yan sandan Isra'ila su 700 da kuma sojoji 200 ne suka halarci wajen ranar Litinin lokacin da ake rushe gidajen a kauyen Wadi Hummus, a kusa da Sur Baher.

Sun isa kauyen ne da karfe 2:00 na dare, tare da motocin rusau suka rushe gida 10 da Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya kamata a rushe.

Falasdinawa 9 da suka rasa muhallansu dai 'yan gudun hijirar ne kuma a cikinsu akwai yara biyar, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Labarai masu alaka