Magidanci ya 'kashe' kaninsa bayan da ya daba masa wuka a Kano

Kisan kai
Bayanan hoto,

Rundunar 'yan sandan jihar Kano sun mika batun ga 'yan sandan ciki na jihar

Rundunar 'yan sanda jihar Kano ta ce da misalin karfe tara na dare na ranar Juma'a sun samu kiran waya inda aka sanar da su labarin wani magidanci ya caka wa kanensa wuka jini na ta zuba.

Mutumin mai shekara 57 ya caka wa kanen nasa mai shekara 20 wuka mai kaifi a kirjinsa, a unguwar Kofar Ruwa da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano.

A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta fitar, matashin ya mutu ne bayan an garzaya da shi zuwa asibitin Murtala da ke birnin.

Tuni rundunar ta ce ta kame mutumin da take zargin sannan ta samu wukar da ya aikata laifin da ita.

Sanarwar ta kara da cewa rundunar 'yan sandan ta mika batun ga 'yan sandan ciki domin binciken hakikanin abin da ya faru.

Ana dai yawan samun irin wannan yanayi na dan uwa ko kuma 'yar uwa ta kashe danginta.

Ko a 'yan watannin da suka gabata wata matashiya 'yar shekara 19 ta daba wa yayanta mai shekara 30 wuka inda ta kashe shi.

Sa-in-sa ce dai ta kaure tsakanin matashiyar da yayan nata ana cikin shagalin bikin wata 'yar uwar tasu daban.

Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fitar ta ce matashin ya nemi da a dakatar da kide-kiden da ake yi a wurin bikin ne, al'amarin da bai yi wa kanwar tasa dadi ba, inda ta dauko wuka ta daba masa a wuya.