'Yan Shi'a sun kashe mana babban jami'i – 'Yan sanda

Wata yarinya da aka dauko ranga-ranga Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Mabiya Shi'a na zargin 'yan sanda sun far musu inda suka kashe musu mutum 11 da jikkata 30

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta zargi mabiya Shi'a da kashe wani mataimakin kwamishinan 'yan sanda DCP Usman A.K Umar a Abuja.

A ranar Litinin ne 'yan sanda suka yi artabu da 'yan Shi'a masu zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim el-Zakzaky, wanda ya kwashe fiye da shekara hudu a tsare.

A wata sanawar da rundunar ta aike wa BBC, ta ce masu zanga-zangar ne suka harbi jami'in daga nan ne ya ji munanan raunuka wadanda kuma suka yi ajalinsa bayan an garzaya da shi asibiti.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Har ila yau rundunar ta kuma ce masu zanga-zangar sun jikkata wasu jami'anta biyu da wani ma'aikacin gidan talabijin na Channels TV.

Mai magana da yawun kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) Ibrahim Musa ya musanta wadannan zargin inda ya ce 'yan sanda ne suka "kashe jami'insu da kansu lokacin da suke harbi kan mai uwa da wabi."

Daga nan ya ce 'yan sandan sun kuma "kashe" masu mutum 11 sannan suka jikkata wasu 30 a lokacin zanga-zangar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Abdullahi
  • Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron bayanin wani dan Shi'a mai zanga-zanga

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da yadda jami'an tsaron Najeriya suka yi "amfani da bindiga" wajen tarwatsa masu zanga-zanga wadanda ta ce suna amfani da damarsu ta "fadin albarkacin bakinsu ne kawai."

A wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, Amnesty ta yi kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike kan harbe-harben da 'yan sanda suka yi domin hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Sai dai tuni aka datse manyan hanyoyin da ke hada tsakiyar birnin na Abuja da fadar shugaban kasa da majalisar dokoki da kuma yankunan da kotuna suke.

Ita ma hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta zargi masu zanga-zangar da kona musu motocin kai dauki guda biyu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NEMA, Sani Datti ya fitar, ta ce "'Yan Shi'a ne suka kona motocinmu na taimakon gaggawa guda biyu da ke kan titin Ahmadu Bello Way a birnin Abuja."

Buhari ya ce babu hannunsa a ci gaba da rike Zakzaky

A ranar Juma'a ne dai mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar da wata sanarwa, inda ya nemi 'yan kungiyar IMN su daina hawa titunan birnin kasar suna "tayar da zaune tsaye".

Sanarwar dai ta kara da cewa "bai kamata a rinka dora wa Shugaba Buhari laifin ci gaba da rike jagoran kungiyar, Sheikh Zakzaky ba."

Mai magana da yawun shugaban ya ce, kasancewar batun jagoran na IMN na gaban kotu a jihar Kaduna, "bai kamata a zargi gwamnatin tarayya da ci gaba da rike shugaban mabiya mazhabar Shi'a ba."

Malam Garba Shehu ya kara da cewa "fadar gwamnatin Najeriya na jan hankalin mabiya mazhabar ta Shi'a da su jira hukuncin da kotun Kaduna inda aka gurfanar da Sheikh Zakzaky za ta yanke, maimakon tayar da zaune tsaye."

Sanarwar ta kara da cewa "ko kadan bai dace ba a rinka tayar da yamutsi alhali batun da ake magana a kai yana gaban kuliya."

Labarai masu alaka