Abin da ya sa muka ajiye makaman yaki a Zamfara - 'Yan bindiga

Bello Matawalle tare da Laftanal Janar Tukur Buratai Hakkin mallakar hoto @Bellomatawalle1
Image caption Gwamna Matawalle kenan (daga hagu) lokacin da ya kai ziyarar aiki ga Janar Buratai a ranar Alhamis kan ayyukan tsaro a jihar Zamfara

'Yan bindiga a jihar Zamfara sun bayyana dalilan da suka sa suka "sassauta tutar yaki" bayan wani taro da aka yi tsakanin mahukunta da kuma shugabannin 'yan bindigar a garin Birnin Magaji.

Wannan ya biyo bayan yunkurin gwamnatin jihar ne na samar da zaman lafiya bayan daruruwan mutane sun rasa rayukansu aka kuma raba wasu da mahallansu sakamakon hara-haren 'yan bindiga.

Wasu daga cikin jagororin 'yan bindigar sun bayyana cewa yanzu zaman lafiya suke bukata su ma, har ma suka bukaci malamai da su dage da addu'a.

Daya daga cikinsu da ya yi magana a wurin taron ya ce sun gama shiryawa tsaf domin kone wasu garuruwa kurmus kafin a samu sulhun.

"Kafin a ramntsar da gwamna akwai gari 80 da aka saka a layi cewa da zarar an sha ruwa (in an gama azimin Ramadana) za mu yi lebur da su, ba soja ba ko wane ne a wajen, kuma garin Birnin Magaji shi ne na farko."

Ya kara da cewa: "Bayan da Allah ya kawo mai girma gwamna ya yi magana a rediyo, bai san mu ba mu san shi ba. Ya yi magana ranar Laraba mu kuma Asabar muka sassauta tutocin yaki.

"Addu'a muke bukata daga malamanmu, sannnan su kuma dattijai su saka albarka. Babu wata matsala insha'allahu indai har kun rike amana."

'Bai kamata a yi sulhu ba'

Hakkin mallakar hoto @AA_Yari2015
Image caption Abdulaziz Yari ya sauka daga kujerar gwaman Zamfara a 2019

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar ya ce an sha yin sasanci da 'yan fashi amma hakan bai kawo karshen kashe-kashe ba.

"Sasanci, na yi na daya na yi na biyu kuma amma na uku na ce ba zan sake ba saboda hakan bai hana abin da ake a Zamfara ba na satar mutane da kasha-kashen mutane da dabbobin jama'a."

"Dole idan za ka yi sasanci sai an fito a fuskar fin karfi, cewa na fi ka karfi dole ka mika wuya," in ji Yari.

'Sulhun yana tasiri'

A makon da ya gabata rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ta bakin kakakinta SP Muhammad Shehu ta shaida wa BBC cewa sulhun da ake yi "yana tasiri".

Kuma ya zuwa yanzu masu satar jama'a don karbar kudin fansa sun sako mutane da dama sakamakon zaman sasantawar, in ji shi.

Ya ce a bisa yarjejeniyar wadda Kwamishinan 'yan sandan jihar Usman Nagoggo da hadin gwiwar gwamnatin jihar suka shirya, 'yan kungiyar sa-kai sun saki Fulani 25 da suka kama.

Ya ce Kwamishinan ne da kansa ya je har garin Dansadau ya karbi mutanen ya je ya damka su ga gwamnan jihar.

Kwana daya bayan wannan kuma aka karbo wasu mutanen su 15, wadanda su kuma Hausawa ne a garin Shinkafi, in ji kakakin.

'Mun yafe wa kowa'

Hakkin mallakar hoto @Bellomatawalle1
Image caption Gwamna Bello Matawalle (daga hagu) yayin da yake ganawa da Shugaba Buhari kan harkokin tsaro a watan Yuni

Sabon Gwamna Bello Matawalle wanda ake ganin yana daukar matakai ne irin wadanda aka dauka a baya, ya shaida wa BBC cewa matakan sun fara haifar da sakamakon da ake so.

Ya ce sakamakon matakin na sulhu yanzu an sako mutum 335 ba tare da masu garkuwa da su sun bukaci a biya wasu kudin fansa ba.

"Mun ja layi cewa duk mai laifi kowa ya ajiye makami ba tare da kuma ganin lafin wani ba," a cewar Matawalle.

Labarai masu alaka