'Haramta kungiyar 'yan Shi'a ta IMN ba mafita ba ce'

Mabiya Shi'a dauke da dan uwansu ranga-ranga Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Mabiya Shi'a na zargin 'yan sanda sun far musu inda suka kashe musu mutum 11 da jikkata 30

Masana a Najeriya musamman masu lura da yadda al'amura ke gudana na yi wa rade-radin da ake yi cewa gwamnatin Najeriya ka iya 'haramta' kungiyar 'yan Shi'a ta IMN.

A ranar Juma'a ne dai 'yan Shi'ar suka yi zargin cewa 'yan sanda sun 'bude' musu wuta yayin wata zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh El-zakzaky wanda ya ke hannun gwamnati tun 2015.

Akalla mutum 14 ne suka mutu a yamutsin, inda aka kashe 'yan Shi'a 11 da wani babban jami'in 'yan sanda guda da kuma dan jarida wanda harsashi ya same shi.

Lamarin ya kuma yi sanadiyyar kona wasu motoci tare da kawo tsaiko a zirga-zirgar jama'a.

Masu lura da al'amura irin su Mannir Dan Ali, shugaban kamfanin jaridar Daily Trust na ganin beken haramta kungiyar inda ya ce "ba ya tsammanin haramta kungiyar ta IMN zai samar da zaman lafiya sai dai ma ya kara ta'azzara yanayin tsaro."

Ya kara da cewa "hanyar da ya kamata gwamnati ta bi wajen warware al'amarin ita ce ta bin umarnin kotu."

Sai dai ya bai wa gwamnatin shawara cewa "idan gwamnati ta bi umarnin kotu ta saki Elzakzaky tana da karfin ikon da za ta iya masa daurin talala domin takaita zurga-zurgarsa."

Tun a shekarar 2015 ne ake tsare da Sheikh Zakzaky bayan wani hari da jami'an tsaro suka kai wa magoya bayansa a Zariya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 300.

Kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta duniya ta bayyana alhininta kan kisan Mista Owolabi, sannan ta nemi da a gudanar da cikakken bincike.

Tun lokacin ne kuma mabiyansa ke ta zanga-zangar neman a sako shi, suna masu zargin cewa "yana cikin mummunan yanayin rashin lafiya".

Lamarin da yake kuma kaisu ga yin taho-mu-gama da jami'an tsaro akai-akai wanda ke haifar da hasarar rayuka da ta dukiyoyi.

Ko a farkon watannan sai da suka kutsa kai majalisar dokokin kasar domin neman ta sa baki a saki shugaban nasu, lamarin da ya kai dage zaman majalisar da kuma harbe wasu magoya bayansu.

Matsayar 'yan sanda

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta zargi mabiya Shi'a da kashe wani mataimakin kwamishinan 'yan sanda DCP Usman A.K Umar a Abuja.

A wata sanawar da rundunar ta aike wa BBC, ta ce masu zanga-zangar ne suka harbi jami'in, daga nan ne ya ji munanan raunuka wadanda kuma suka yi ajalinsa bayan an garzaya da shi asibiti.

Har ila yau rundunar ta kuma ce masu zanga-zangar sun jikkata wasu jami'anta biyu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Abdullahi
  • Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron bayanin wani dan Shi'a mai zanga-zanga

Sai dai mai magana da yawun kungiyar ta 'yan Shi'a Ibrahim Musa ya musanta wadannan zarge-zargen inda ya ce 'yan sanda ne suka "kashe jami'insu da kansu lokacin da suke harbi kan mai uwa da wabi."

Daga nan ya ce 'yan sandan sun kuma "kashe" masu mutum 11 sannan suka jikkata wasu 30 a lokacin zanga-zangar.

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da yadda jami'an tsaron Najeriya suka yi "amfani da bindiga" wajen tarwatsa masu zanga-zanga wadanda ta ce suna amfani da damarsu ta "fadin albarkacin bakinsu ne kawai."

A wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, Amnesty ta yi kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike kan harbe-harben da 'yan sanda suka yi domin hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Ita ma hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta zargi masu zanga-zangar da kona musu motocin kai dauki guda biyu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NEMA, Sani Datti ya fitar, ta ce "'Yan Shi'a ne suka kona motocinmu na taimakon gaggawa guda biyu da ke kan titin Ahmadu Bello Way a birnin Abuja."

Masu lura da al'amura sun dade suna kokawa da jan hankalin gwamnati kan ta dauki matakan da za su kawo karshen wannan rikici ganin yadda yake haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi.

Labarai masu alaka