Za a 'gaggauta' tasa keyar 'yan ci-rani daga Amurka

Donald Trump Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Donald Trump na son sanya batun 'yan ci-rani a kan gaba a batutuwan yakin neman zabensa

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za a kara azama ko kuma gaggauta yadda kasar ke mayar da 'yan ci-rani gida.

Gwamnatin Donald Trump dai na kokarin kara fadada karfin ikon jami'an kula da shige da fice wajen basu ikon tasa keyar 'yan ci-rani domin barin Amurka ba tare da sun gurfanar a gaban kotu ba.

Wannan sabon tsarin na gaggauta tasa keyar baki zai iya shafar duk wanda ya shiga Amurka ba bisa ka'ida ba kasa da shekaru biyu da suka gabata kuma ko a ina kuwa aka kama shi a fadin kasar.

A da, bakin da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba kasa da makonni biyu da aka tsare tsakanin kilomta 160 daga iyakar Amurka ne kadai za a iya gaggauta tasa keyarsu ba tare da an gurfanar da su gaban alkali ba.

Ma'aikatar kula da harkokin tsaron cikin gida ta Amurka ta bayyana cewa gaggauta tasa keyar baki ba tare da gurfanar da su gaban alkali ba zai ba ma'aikatar damar tasa keyar da yawa daga cikin bakin da suka kwararo cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

Sai dai wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasar sun bayyana cewa za su kalubalanci shirin a kotu.

A wani bangare kuma Faransa ta ce kasashe takwas na kungiyar Tarayyar Turai sun ce sun amince da ba 'yan ci-ranin da aka ceto daga Tekun Bahar Rum matsuguni sai dai kasar Italiya ta ce ba ta cikinsu.

Kauracewar Italiya na shiga cikin kasashe takwas din da za su yi wannan taimako ba zai rasa nasaba da kasancewar kasar na cikin kasashen da 'yan gudun hijira ko 'yan ci-rani ken yawan kwarara ba.

Labarai masu alaka