Zaben Kano: Abba ya gabatar da shaida 241 kan Ganduje

Ganduje da Abba Gida-Gida
Image caption Jam'iyyar APC da Gwamna Ganduje da kuma INEC sun musanta korafe-korafen PDP da Abba Kabir Yusuf kan zaben

Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben 2019 na jihar Kano ya gabatar da tarin shaida 241 a gaban kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar domin gamsar da ita cewa ba Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya lashe zaben ba.

Abba Yusuf, wanda aka fi sani da "Abba gida-gida", ya sha kayi a hannun Gwamna Ganduje a karashen zaben da aka yi, duk da cewa shi ne kan gaba a zaben farko wanda bai kammala ba.

Sai dai masu sa ido na gida da waje sun soki yadda aka gudanar da karashen zaben suna masu cewa an tafka magudi, zargin da jam'iyyar APC da kuma hukumar zabe suka musanta.

Lauyan masu kara Adeboyega Awomolo wanda shi ne ya gabatar da tarin shaidar gaban kotun ya ce za su yi kokari su kara tattara wasu tarin shaida domin gamsar da kotun, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito.

Mista Awomolo ya bayyana wa kotun cewa cikin shaidar da ya gabatar akwai sahihan sakamakon zabe na mazabun Albasu, Bebeji, Bichi, Danbatta, Garun Malam, Gwarzo, Karaye, Kura, Madobi, Nasarawa, Rano, Rogo, Sumaila, Tudun Wada da Karamar Hukumar Warawa da sauren wurare.

Sai dai lauyoyin da ke kare bangaren Ganduje da jam'iyyar APC wato Offiong Offiong da Ahmad Raji, wadanda duka manyan lauyoyi ne, sun yi watsi da wadannan tarin shaidar da aka gabatar.

Mista Offiong ya bayyana cewa ''Masu kara ba su fito da tarin shaidar karara muka gani ba, jakunkuna kawai aka kawo, muna so muga asalin abubuwan da ke cikin jakunkunan.''

Sai dai Mai Shari'a Halima Shamaki ta yi watsi da batutuwan Mista Offiong inda ta amince da takardun sakamakon zaben a matsayin shaidu kuma ta dage sauraren karar zuwa Talata 23 ga watan Yuli.

NAN ya bayyana cewa ana sa ran shaidu kusan 785 za su hallara gaban kotu domin bayar da shaida ga duka bangarorin APC da PDP kan zaben gwamnan da aka gudanar a watan Maris din da ya gabata a jihar.

Hakkin mallakar hoto Facebook/Abba
Image caption Abba Kabir ya yi zargin cewa magudi Ganduje da APC suka yi masa da hadin bakin INEC

Abba Kabir Yusuf da kuma jam`iyyarsa ne suka shigar da karar bisa zargin cewa zaben cike yake da magudi da kuma aika-aikar `yan bangar siyasa.

Haka kuma masu karar sun bukaci kotu ta yi watsi da sakamakon zaben da aka yi, zagaye na biyu, wanda aka fi sani da "Inconclusive," bisa zargin cewa babu tsarin Inconclusive a cikin dokar zabe.

Abba Kabir Yusuf da kuma jam`iyyarsa na karar Hukumar Zabe ta Kasa, INEC da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne, amma sun musanta zarge-zargen na PDP.

Kotun dai tana da kwana 180 ne ta yanke hukunci daga ranar da aka shigar da karar. A ranar 11 ga watan Afrilun 2019 ne Abba ya shigar da karar.

Ke nan kwanaki 78 ya rage ita wannan kotu ta kammala shari'ar domin yanke hukunci.

Yaushe za a kammala shari'ar?

Barrister Audu Bulama Bukarti ya yi wa BBC bayanin abubuwan da za su faru daga ranar 13 ga watan Yuli idan kotu ta koma zamanta kamar haka:

  • Masu kara za su gabatar da shaidunsu
  • Daga nan kuma sai a bai wa wadanda ake kara su ma su gabatar da nasu shaidun
  • Kotun za ta saurari abin da ake kira jawaban karshe, inda wadanda ake kara za su fara jawabin karshen
  • Daga nan ne kuma sai a bai wa bangaren masu kara su gabatar da nasu jawabin na karshe
  • Kotun za ta sake bai wa wadanda ake kara damar mayar da martani kan jawabin karshe da masu kara suka yi
  • Bayan sauraron jawaban karshe da martani sai kotu ta sa ranar yanke hukunci.

Daya daga cikin hukunci uku da kotu za ta iya yankewa

  • Kotu za ta iya korar karar da Abba Kabir Yusuf, inda za ta tabbatar da Gwamna Ganduje da cin zabe
  • Kotu za ta iya ayyana Abba Kabir Yusuf da wanda ya ci zabe
  • Kotun za ta iya soke zaben domin a sake

Idan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben ta yanke bai gamsar da daya daga cikin bangarorin ba, sai su garzaya kotun daukaka kara.

Yaushe za a yanke hukunci?

Ita dai wannan kotun ta sauraron kararrakin zaben na da kwanaki 180 ta yanke hukunci daga ranar da aka shigar da karar.

Kotun Daukaka Kara na da kwana 60 ta yanke hukunci, inda ita ma Kotun Koli take da kwanakin 60 ta yanke nata hukuncin.