Ba ma yi wa 'yan sanda katsalanda kan Shi'a - Sojoji

Burutai
Image caption Rundunar Sojin Najeriya ta ce ba ta da hannu a rikicin Shi'a

Rundunar sojin Najeriya ta ce har yanzu gwamnati ba ta gayyace ta ba domin kwantar da tarzoma dangane da batun zanga-zanagr da 'yan Shi'a ke yi ta neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim Elzakzaky.

Mai magana da yawun sojojin kasar, Col. Onyema Nwachukwu ne ya fadi haka yayin hira da manema labarai bayan kammala wani taron manema labarai kan yanayin tsaro a kasar.

Rundunar sojojin ta ce batun 'yan Shi'a abu ne da ya shafi 'yan sanda saboda haka ba za su yi musu katsalanda ba.

Kanal Onyeama ya bayyana abun da ya faru lokacin zanga-zangar da 'yan Shi'a suka yi abin takaici ne.

Sojojin sun ce sun mayar da hankali ne wajen yaki da matsalolin tsaro a sauran sassan kasar.

Dangane da batun yawaitar satar jama'a da kashe su, Kanal Onyeama ya ce sun kashe akalla masu satar jama'a 75 a watanni biyu da suka wuce.

Ya kuma kara da cewa sun kama da tsare masu satar jama'a 45 sannan sun ceci mutanen da aka yi garkuwa da su guda 52.

Har wa yau, sojojin sun ce sun kama masu garkuwa da jama'a 14 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda kuma suka ceci wadanda aka yi garkuwa da su guda 7.

Kanal Onyeama ya kara da cewa sun samu nasarar tseratar da shanu fiye da 3,000 daga hannun barayin shanun.

Labarai masu alaka