Tarayyar Turai ta ce Boris Johnson na da jan aiki a gabansa

Boris Johnson is seen outside his office after being announced as Britain's next prime minister in London on 23 July 2019 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Boris Johnson tsohon sakataren harkokin wajen Birtaniya ne

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi gargadin cewa Firaministan Birtaniya mai jiran gado Boris Johnson yana fuskantar lokaci mai cike da kalubale, a yayin da kungiyar ke mayar da martani kan zabensa a matsayin sabon shugaban Jam'iyyar Conservative.

Mista Johnson yana da kalubale mai jiransa da zarar ya hau kujerar domin jagorantar ficewar Birtaniya daga Tarayyar gabanin wa'adin da aka sanya na ranar 31 ga watan Oktoba.

Ya ce yana son ya sabunta tattaunawa kan yarjejeniyar, ya kuma yi watsi da mafi yawan abubuwan da Firaminista mai barin gado Theresa May ta shirya a baya.

Amma shugabannin EU sun ce batun cewa a sake tattaunawa ma bai taso ba.

Sai dai sabuwar Shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta ce a shirye take ta bai wa Birtaniya wata damar ta sake dage tattaunawar Brexit, idan har Birtaniya ta zo da sabbin dalilai sahihai.

Da take taya Mista Johnson murna, Mrs von der Leyen ta ce: "Akwai batutuwa daban-daban kuma masu wahala da ake bukatar magance su tare.

"Akwai kalubale sosai a gabanmu. Ina ganin yana da muhimmanci kwarai a gina wata kakkarfar dangantaka saboda hakkinmu ne mu samar da abu mai kyau ga mutanen nahiyar Turai da kuma Birtaniya."

Shugaban Amurka Donald Trump ya taya shi murna a shafin Twitter.

An samu karin martani daga sassan Turai daban daban:

A Jamus, Shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta taya Boris Johnson murna, tana mai cewa za ta ci gaba da ganin an samu "kyakkyawar" dangantaka da Biratniya.

A wata sanarwa, jam'iyyarta ta CDU ta ce tana fatan Mr Johnson "ya kawo manufofi masu kyau domin amfanin Birtaniya da kauce wa fitar da kasar daga Turai ta kowacce hanya".

Shugabannin kamfanonin Jamus ma sun yi gargadin cewa barazanar ficewa ba tare da yarjejeniya ba za ta shafi bunkasar tattalin arziki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yaba wa Firaminista mai barin gado Theresa May kan yadda "ta nuna dattaku da kwarin gwiwa" da kuma yadda ba ta taba "kawo tsaiko ga ayyukan Tarayyar Turai ba".

Sannan ya ce yana fatan yin aiki tare da sabon shugaban kan batun ficewar kasar daga Tarayyar Turai da kuma sauran batutuwa masu muhimmanci.

Ministan cikin gida na Italiya kuma shugaban jam'iyyar Lega (League), Matteo Salvini, ya wallafa a Twitter cewa: "Aiki ya yi kyau #BorisJohnson. Ganin yadda ake kwatanta shi da cewa ya fi "jam'iyyarmu ta Lega hadari" ya sa na kara kaunarsa."