Ko kun san waye Shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi?

Beji Caid Essebsi Hakkin mallakar hoto AFP

Fadar shugaban kasar Tunisia ta sanar da mutuwar shugabanta Beji Caid Essebsi, wanda ya mutu yana da shekara 92.

Shi ne shugaban kasar da ya fi kowa tsufa a duniya. An kwantar da shi a asibiti ranar Laraba amma jami'ai ba fadi dalilin rashin lafiyar tasa ba.

A shekerar 2014 ne Mista Essebsi ya lashe zaben farko na kasa tun bayan boren kasashen Larabawa.

Mista Essebsi ya kuma kwanta a asibiti a watan da ya gabata bayan fama da abin da jami'ai suka kira "rashin lafiya mai tsanani."

Ba su yi karin bayani kan batun ba. Firai Minista Youssef Chahed, wanda ya ziyarce shi a asibiti, ya roki mutane da su daina yada "labaran karya" a kan halin da shugaban ke ciki.

A tsarin kundin tsarin mulkin kasar, Mista Chahed zai iya zama shugaban kasa na tsawon kwanakin da ba za su wuce 60 ba ko kuma zuwa lokacin da za a zabi sabon shugaba.

A farkon shekarar nan ne ya sanar da cewa ba zai tsaya a zaben da za a sake yi a watan Nuwamba ba.

A wani taro ya shaida wa jam'iyyarsa ta Nidaa Tounes cewa ya kamata wani mai jini a jika ya karbi ragamar. Ya ce lokaci ya yi da "za a bai wa matasa dama."

Mista Essebsi tsohon lauya ne da ya yi karatu a birnin Paris na Faransa.

A lokacin da yake dan siyasa na tsawon lokaci ya kuma yi ministan harkokin cikin gida da kuma kakakin majalisar wakilai.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty

A shekarar 2011 ne aka hambarar da tsohon shugaban Tunisiya Zine el-Abedine Ben bayan shafe shekara 23 a kan mulki.

Tun sannan ake jinjinawa Tunisiya kasancewarta kasar da ita kadai ta hau turbar dimokradiyya bayan boren kasashen Larabawa.

Sai dai a shekarun baya-bayan nan kasar ta sha fama da hare-haren masu ikirarin jihadi da kuma tabarbarewar tattalin arziki, inda yawan marasa aikin yi ke ta'azzara.

Labarai masu alaka