Amurka ta sanya wa wasu 'yan Najeriya takunkumi

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Najeriya da dama na zuwa Amurka domin shakatawa, aiki ko kuma harkokin kasuwanci

Amurka ta bayyana cewa ta saka takunkumi ga wasu 'yan Najeriya wadanda ta ce suna kawo tsaiko ga tafarkin dimokuradiyyar kasar.

Wannan takunkumi, wanda zai shafi har wadanda suke da hannu a tayar da zaune tsaye a lokacin zabe, zai hana su samun takardar izinin shiga Amurka.

Babu wata sahihiyar hanya da za a iya cewa Amurka ta bi domin zakulo wadanda ake ganin wannan takunkumin zai shafa duk da cewa ba a wallafa sunayensu ba.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta bayyana cewa wannan takunkumin zai shafi wasu daga cikin 'yan Najeriyar ne kawai, ba wai gwamnatin kasar ba ko kuma gaba daya jama'ar kasar.

Wannan ba shi ne karon farko ba da Amurkar ke nuna damuwarta kan yadda wasu ke kawo tasgaro ga tsarin dimokuradiyyar Najeriyar ba.

Ko a ziyarar da tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya kai kasar kafin zaben 2015, ya sha alwashin cewa duk wanda aka samu da hannu dumu-dumu wajen tayar da hargitsi lokacin zabe, Amurkar ba za ta ba shi takardar izinin shiga kasar ba.

Sai dai ko a bayan zaben 2015 din, Amurkar ba ta cika wannan alkawarin na ta ba.

Wani tsohon mai bayar da shawara ga ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya shaida wa BBC cewa matakin da aka dauka a yanzu kamar alamu ne na tabarbarewar dangantaka tsakanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya.

Sanarwar wannan takunkumin kan takardar izinin shiga Amurka ga wasu 'yan Najeriya na zuwa ne a ranar da Shugaban Najeriyar ya aika da sunayen wadanda yake so a matsayin ministocinsa ga majalisar dattawan kasar domin tantancesu.

Labarai masu alaka