Yadda Yahya Jammeh ya sa aka 'kashe' 'yan ci-rani 50

Yahya Jammeh Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yahya Jammeh ya shafe shekara 22 yana mulkar Gambiya kafin ya fadi a zabe

Wani soja na kasar Gambiya ya amsa laifin cewa yana daya daga cikin wadanda suka kashe 'yan gudun hijira kusan 50 bisa umarnin Tsohon Shugaban kasar Yahya Jammeh, wanda a wancan lokacin yana ganin kamar mutanen sun zo su yi masa juyin mulki ne.

Sojan ya bayar da shaida ne gaban wani kwamiti da ke binciken irin barnar da aka yi a mulkin Yahya Jammeh na shekaru 22.

Tun a baya, sojan ya bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka kashe wani dan jarida a 2004 mai suna Deyda Hydara wanda ya ce Mista Jammeh ne ya bayar da umarnin aiwatar da kisan.

Tsohon shugaban kasar Gambiya ya sha musanta hannu a kisan 'yan ci-ranin.

Sai dai wani soja wanda mamba ne a runduna ta musamman da Yahya Jammeh ke jagoranta, ya shaida wa hukumar bincike ta kasar yadda aka kashe wasu mutum 50 - mafiya yawansu 'yan kasar Ghana.

Laftanar Malick Jatta, ya ce Yahya Jammeh, wanda yanzu haka ke gudun hijira a kasar Equatorial Guinea, shi ne ya bayar da umarnin kashe mutanen.

Wadannan bayanai sun yi daidai da binciken da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi.

Rahotanta ya ce 'yan ci-ranin wadanda suka fito daga kashashen Yammacin Afirka domin tsallakawa zuwa Turai, an tsaresu sannan aka kashe su bayan da kwale-kwalen da suka shiga daga Senegal ya isa Gambiya.

Labarai masu alaka