Muna kira da a saki 'yan Shi'a da aka kama - HRW

Shiites
Image caption 'Yan Shi'a sun ce babu gudu babu ja da baya kan neman a saki shugabansu Elzakzaky

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Human Rights Watch, HRW, ta bukaci jami'an tsaron Najeriya da su yi amfani da tanade-tanaden majalisar Dinkin Duniya wajen amfani da karfi fiye da kima ta hanyar bindiga.

A ranar Litinin ne dai mabiya mazahabar Shi'a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky suka yi zanga-zangar neman a sake shi inda suka hadu da fushin 'yan sanda al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan kungiyar 11 da dan sanda daya da kuma dan jarida guda.

A wata sanarwa da kungiyar HRW ta fitar ta hannun mai babbar mai bincikenta, Anietie Ewang, ta ce dokokin Majalisar Dinkin Duniyar dai sun ce 'jami'an tsaro su yi amfani da "hanyoyin da ba na karfi ba da farko wajen warware takaddama kafin yin amfani da karfin", kuma a duk lokacin da amfani da bindiga ya zama wajibi to jami'an tsaron su yi amfani da karfin dai-dai kima yadda ba za su wuce gona da iri ba.

Kungiyar ta kara da cewa Majalisar ta Dinkin Duniya ta kuma ce "za a iya amfani da bindiga ne kawai idan rashin yin amfanin da ita zai janyo asarar rayuka."

Daga nan kuma kungiyar HRW ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta gudanar da sahihin bincike kan hakikanin abin da ya faru a ranar 22 ga watan Yuli domin hukunta duk wadanda aka samu da laifi.

Har wa yau, Human Rights Watch ta yi kira ga gwamnati da ta saki masu zanga-zangar da 'yan sanda suka ba bisa ka'ida ba sannan kuma wadanda suka jikkata a cikinsu a kai su asibiti.

sanarwar ta ce gwamnatin Najeriya ta dade tana amfani da karfi fiye da kima a kan 'yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria tun 2015, lokacin da sojojin kasar suka far wa gidan jagoran kungiyar a Zariya a watan Disamba.

Tun lokacin ne suke tsare da jagoran kungiyar, Sheikh Ibrahim El-zakzaky da mai dakinsa. Sojojin dai sun yi zargin cewa 'yan kungiyar sun tare wa hafsan sojin kasar hanyar wucewa.

Anietie Ewang ta ce sun gano yadda sojoji da 'yan sanda suka kashe 'yan Shi'a 63 a watan Oktoba 2018

Sannan an kashe 'yan kungiyar 110 duk a kokarin neman a sakin jagoransu a jihohin Kaduna da Kano da Katsina da Yobe da Plateau da Sokoto da kuma Abuja.

Daga karshe Ewang ta ce "Gwamnatin Najeriya ta dakatar da amfani da karfi a kan masu zanga-zanga,"

Da ma kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International Kungiyar ta yi Allah-wadai da yadda jami'an tsaron Najeriya suka yi "amfani da bindiga" wajen tarwatsa masu zanga-zanga wadanda ta ce suna amfani da damarsu ta "fadin albarkacin bakinsu ne kawai."

A wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, Amnesty ta yi kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike kan harbe-harben da 'yan sanda suka yi domin hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Labarai masu alaka