Yadda matashi ya kashe mahaifinsa mai shekara 70

'Yan sanda
Image caption Jami'an tsaron Najeriya na fatan kawo karshen masu laifi

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar wa BBC cewa da misalin karfe 12 na ranar Talata ne dai matashin mai shekara 25 ya bi mahaifin nasa mai shekara 70 zuwa gona, inda ya sa kotar fartanya ya buge shi.

SP Jinjiri ya kara da cewa an tarar da dattijon a kwance magashiyyan a gonar tasa, ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da shi zuwa asibiti, inda ya ce ga garunku nan.

Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar ta Jigawa ta ce ta cafke matashin wanda ya tsere bayan ya 'tafka ta'asar'.

SP jinjiri ya ce bayan tambyoyi da suka yi wa matashin sun fahimci cewa yana cikin halin maye saboda haka ana kyautata zaton kwaya ce ta debe shi ya yi 'aika-aikar'.

Yawan kashe-kashe a tsakanin dangi a Najeriya

Kusan za a iya cewa kisa a dangi, inda ake samun yanayin da mata ke kashe mai gida ko kuma mai gida ya kashe matar ko kuma dan uwa da 'yar uwa ko ma da ya kashe mahaifi ko mahaifiyarsa, ya dade yana faruwa a Najeriya musamman a arewacin kasar.

Yawaitar al'amarin na sa mutane tunanin yadda zamani ya lalace kasancewar abu ne da 'yan baya ka iya cewa sabo ne.

Ga wasu lokutan da aka yi irin wadannan kashe-kashe na cikin dangi a watan Yulin nan:

  • 23 Yuli 2019 - Matashi ya kashe mahaifinsa a Jigawa
  • 19 Yuli 2019 - Magidanci dan shekara 57 ya kashe kaninsa dan shekara 20 a Kano
  • 6 Yuli 2019 - Matashiya mai shekara 19 ta kashe yayanta mai shekara 30 a Kano