Saudiyya ta haramta wa 'yan DR Congo zuwa Hajji

hajj Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce ba za ta bai wa 'yan kasar Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo izinin shiga kasarta don yin aikin hajji ba.

Ma'aikatar ta ce ta yanke hukuncin ne bayan da Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ayyana dokar ta baci kan lafiya a kasar ta DR Congo wacce ke fama da annobar cutar Ebola tare da nuna damuwa kan hankan.

"An dakatar da bai wa 'yan Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo biza domin a kare sauran mahajjata daga kamuwa da annobar," a cewar ma'aikatar.

A farkon wannan watan ne Saudiyya ta ce mutum 410 ne za su je aikin hajji da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, kamar yadda wani jagoran addinin Musulunci na Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo Imam Djuma Twaha, ya shaida wa BBC.

"Akwai mutanen da suka shafe shekaru suna shirin zuwa hajjin nan, wasu ma har shekara 10 suke suna tara kudi dala 4,250 don yin wannan ibada mai girma a Makkah," a cewarsa.

A ranar 17 ga watan Yuli ne WHO ta ayyana dokar ta baci kan lafiya a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, amma ta nemi kasashen duniya da ka da su dauki matakin hana tafiye-tafiye.