Ido ko hannu ba shi yake rike minista ba- Muntari Saleh
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Makafi: 'Za mu bayar da mamaki a zabe mai zuwa'

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Sakataren kungiyar makafi ta Arewacin Najeriya Muntari Saleh ya yi Allah wadai da jerin sunayen ministocin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari.

A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saki jerin sunaye 43 na ministocin Najeriya.

Muntari Saleh ya ce ya kamata mutane masu nakasa su samu wakilci a jerin ministocin.

Ya kara da cewa nakasa ba kasawa ba ce, tun da ba ido ko hannu ne ke rike minista ba, ilimi ne, "idan neman kuri'a ne sai a neme mu amma idan dadi ya zo sai a manta da mu," a cewarsa.

Labarai masu alaka