Dani Ceballos ya koma Arsenal daga Madrid

Dani Ceballos Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dani ya koma Real Madrid ne daga Real Betis a shekarar 2017

Dan wasan tsakiyar kungiyar Real Madrid Dani Ceballos ya koma Arsenal a matsayin aro har zuwa karshen kakar badi.

Dan wasan mai shekara 22 ya taka wa Madrid leda sau 56 tun bayan da ya koma kungiyar a shekarar 2017 daga Real Betis.

Kocin Arsenal Unai Emery ya ce: "Muna farin cikin dawowar Dani. Dan kwallon yana da kwarewa sosai."

Haka zalika Arsenal ta shirya sayen William Saliba daga kungiyar AS Saint-√Čtienne ta Faransa wanda ake zaton farashinsa zai kai fam miliyan 27.

Saliba ya bayyana farin cikinsa game da komawa Arsenal duk da cewa Tottenham ta yi zawarcinsa.

Karanta wasu karin labarai

Labarai masu alaka