An kara wa sojan da ya mayar da miliyan 15 da ya tsinta girma

Bashir Umar wanda ya tsinci makudan kudi a yayin da yake sintiri Hakkin mallakar hoto Nigerian Airforce/Twitter
Image caption Bashir Umar wanda ya tsinci makudan kudi a yayin da yake sintiri a Kano

Rundunar sojan saman Najeriya ta kara wa wani jami'inta wanda ya mayar da naira miliyan 15 (kimanin Dala 41,500) da ya tsinta, karin girma har mataki biyu.

Jami'in mai suna Bashir Umar na cikin Tawagar Kar-ta-Kawana ta Mayakan Sama ta rundunar wadda aka aike zuwa filin jirgin sama na Kano da ke arewacin kasar domin tabbatar da tsaro.

A wata sanarwa da ta fitar rundunar sojin saman ta ce Bashir na tare da wani abokin aikinsa ne suna sintiri yayin da ya tsinci damin kudin.

Sai dai maimakon ya danne kudin, rundunar ta ce sai jami'in ya duba jikin takardar da kudin ke nade a ciki inda ya ga lambar wayar mai kayan, ya kuma kira shi.

An kara masa girma ne da mukamin kurtu zuwa kofur, wanda idan ba don haka ba zai iya daukarsa tsawon shekara 10 kafin ya kai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya bayyana.

Haka zalika an bai wa jami'in shaidar yabo.

Babban hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya ce Umar ya nuna "kyakkyawan halin dawo da kudin da ya tsinta wanda hakan yanzu ya yi karanci."

Umar wanda ya halarci taron girmama shi tare da iyayensa ya ce ya mayar da kudin ne ga mai su saboda tasirin dabi'un gidansu da na aikinsa.

A farkon makon nan ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan kasar musamman matasa da su yi koyi da wannan dabi'a," kamar yadda wata sanarwa daga mai magana da yawunsa Femi Adesina ya bayyana.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da jami'ai masu kamanta gaskiya suke mayar da abin da suka tsinta a filayen jiragen saman Najeriya ba.

A watan Agustan bara ma, hukumomi a filin jirgin saman Legas sun karrama masu gadin wajen biyu, wadanda suka mayar da makudan kudi da abubuwa masu tsada da suka tsinta.

Haka ma a watan Satumba, an jinjinawa wani mai share-share kan mayar da wasu kayayyaki masu tsada na wani fasinja da ya yi.

Labarai masu alaka