IS ta dauki alhakin sace ma'aikatan agaji a Borno

Ma'aikatan agaji na Action against Hunger Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar IS reshen Afirka ta Yamma ta dauki alhakin yin garkuwa da ma'aikatan agaji shida a arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar IS din dai ta bayyana haka ne a jaridarta ta al-Naba mai fitowa duk mako a harshen Larabci.

Kungiyar agaji ta Action Against Hunger ta tabbatar da sace ma'aikatanta a makon jiya bayan da wani hoton bidiyo ya bayyana ranar Laraba.

Hoton bidiyon ya nuna ma'aikatan suna rokon gwamnati da sauran kasashen duniya da su nemo hanyoyin sama masu 'yanci.

Ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya, ta bakin mai magana da yawun Shugaba Buhari, ta bayyana cewa tana tattaunawa da kungiyar IS din, amma ba ta bayar da wani karin bayani ba.

Malam Garba Shehu ya bukaci masu garkuwar da su "tausaya" a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sannan ya ce wannan tattaunawar ba iya wadannan ta shafa ba, "har da Leah Sharibu" wadda tana daya daga cikin 'yan mata 'yan makaranta da Boko Haram ta sace daga garin Dapchi na jihar Yobe a watan Maris na 2018.

Kungiyar IS dai ta sha kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya a watannin da suka gabata, inda a mafi yawan lokuta suka kai hari sansanonin sojoji.

Watanni tara da suka gabata ne kungiyar ta kashe wata ma'aikaciyar agaji da ta yi garkuwa da ita a bara.