Kylie Jenner: Matar da ke samun $1.2m a duk sakon da ta wallafa a Instagram

kylie-jenner. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana biyan Kylie Jenner kusan dala miliyan 1.2 a duk sakon da ta wallafa a Instagram

Wani sabon rahoto ya ce ana biyan Kylie Jenner kusa dala miliyan 1.2 a duk wani abu da ta wallafa a Instagram.

Hakan ne ya sa ta zamo wacce aka fi biya sosai cikin mutanen da suka fi yawan mabiya a shafin Instagram a 2019, a cewar kamfanin manhajar da ke wallafa sakonni a madadin mutane Hopper HQ.

Ko a bara ma Kylie - wacce ke da mabiya miliyan 141 - ita ce ta dare jerin, lokacin da aka bayar da rahoton cewa tana samun kusan dala miliyan daya a duk sako daya da ta wallafa wa mabiyanta.

Tsarin da ake bi wajen yin hakan sun hada da duba yawan mabiyan da fitattun mutane ke da su, da kuma yawan yadda aka sake aika abin da suka wallafa ko kuma tsokacin da aka yi a kai.

Mutum ukun da suka zama na gaba-gaba wajen samun kudi a Instagram cikin masu yawan mabiya sun hada da:

  • Kylie Jenner - dala miliyan 1.2million a duk sako daya da ta wallafa
  • Ariana Grande - dala 966,000 a duk sako daya da ta wallafa
  • Cristiano Ronaldo - dala 975,000 a duk sako daya da ya wallafa, duk da cewa shi ne wanda ya fi yawan mabiya a Instagram a duniya, inda yake da mabiya miliyan 177

Selena Gomez da Dwayne 'The Rock' Johnson da Beyoncé da Taylor Swift da Neymarda kuma Justin Bieber su ne sauran wadanda suka biyo bayan wadancan cikin mutum 10.

Ana yawan sukar al'adar biyan fitattun mutane makudan kudade don wallafa wa miliyoyin mabiyansu sako.

Wasu na cewa mabiya na iya sauya dabi'unsu ko ra'ayinsu kan wani abu da aka wallafa, idan sun san cewa wadanda suke bi "sau da kafa" din za su samu kudi kan sakon da suka wallafa.

Masu suka sun kuma ce hakan na sa wa matasa su kasa gane hakikanin abin da suke so ko son cimma a rayuwa idan suka ga irin kudin da fitattun mutane ke samu daga wallafa abu.

Amma wasu na ganin hakan ba wata matsala ba ce a masana'antar fitattun mutane da tuni sana'arsu ke kawo musu miliyoyin fama-famai.

Muna so mu ji ra'ayoyinku. Shin ya kamata a dinga biyan fitattun mutane irin wannan makudan kudade saboda sakonni da suke wallafawa a shafukan sada zumunta?

Me ku ke tunanin kan wannan al'ada?

Labarai masu alaka