'Bai kamata majalisa ta dinga kin yi wa ministoci tambaya ba'

'yAn majalisar dattijan Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan Najeriya na ta tofa albarkacin bakinsu kan yadda majalisar dattijan kasar ta rika kyale wasu daga cikin ministocin da ake tantancewa su fice ba tare da an tambaye su komai ba.

A ranar Juma'a ce aka shiga rana ta uku da majalisar dattijan kasar ke aikin tantance mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika ma ta domin zama ministoci a gwamnatinsa.

Za a iya cewa aikin tantance ministocin na tafiya yadda ya kamata, amma mutane da dama na nuna rashin gamsuwarsu kan yadda majalisar ke kyale wasu daga cikin mutanen domin su tantance su kafin a tabbatar masu da mukamin na minista.

Daga ranar Laraba zuwa Alhamis da ake aikin tantancewar, yawancin wadanda suka bayyana a gaban majalisar ba su amsa ko da tambaya daya ba, a maimakon haka, sai kawai majalisar ta ce su juya su tafi abinsu.

Wannan al'amari ya ja hankulan 'yan Najeriya, inda yawancin wadanda na tattauna da su suka nuna rashin gamsuwarsu da wannan halayya ta majalisar dattijan Najeriya.

A wannan rana ta Jumma'a kuma yini na uku da majalisar dattijan Najeriya ta ci gaba da tantance mutanen da za su zama ministoci a gwamnatin da za ta mulkin Najeriya daga yanzu zuwa shekaru hudu masu zuwa.

Kungiyar Transparency International a Najeriya wadda ke fafutukar kare hakkokin al'umma, ta nuna damuwarta kan hakan.

Shugaban kungiyar Awwal Musa Rafsanjani ya ce ba su gamsu da yadda majalisar dattijan ke aikin tantancewar ba saboda tsarin da suke bi a yanzu ba za a iya gane cancantar wadanda ake tantance su din ba.

"Akwai wadanda da dama 'yan Najeriya ba su ji dadin saka sunayensu a jerin ministocin don ana zarginsu da cin hanci da rashawa. To da a ce majalisa za ta yi aiki bisa tsarin da ya dace da lallai za su tsaya tsayin daka sun ga irin wadannan mutanen ba su samu mukaman minista ba.

"Da yawa daga cikin mutanen har yanzu batun zargin da ake musu na cin hanci yana kotu, amma kuma sai ga shi abin takaici wadanda ya kamata su taya 'yan kasa neman hakkinsu kan irin wannan lamari su ne a kan gaba wajen kauce wa tsarin da ya dace," in ji Rafsanjani.

Labarai masu alaka