Kun san me ya hana gwamnatin Buharin sakin Zakzaky?

Shugaba Buhari da Abubakar Malami Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon ministan shari'a kuma wanda ake tunanin za a sake ba mukamin, ya fadi dalilin da ya sa ya ki amincewa a saki Kanal Sambo Dasuki da kuma Shiekh elZakzaky.

Barista Abubakar Malami, wanda shugaba Buhari ya sake zaba a matsayin minista, yana cikin wadanda suka bayyana a gaban majalisar dattawa a ranar Juma'a domin tantance su.

Batun yadda ya yi fassara da kuma bai wa shugaban kasa shawara kan wasu hukunce-hukuncen kotuna musamman wadanda ake ganin ba su yi wa gwamnati dadi ba, su ne suka fi jan hanakali a tambayoyin da aka yi masa.

An tambayi tsohon ministan na shari'a dalilin da ya sa ya ki amincewa a saki tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Sambo Dasuki da kuma jagoran 'yan Shi'a a Najeriya Malam Ibrahim Zakzaky duk da kotu ta bayar da belinsu amma kuma ake ci gaba da tsare da su.

Malami ya shaida wa BBC cewa ya ce hakkin ofishinsa ne ya kare hakkin 'yan Najeriya ba na wani mutum daya ba.

Ya ce Kundin mulki na Najeriya sashi na 174, ya bayyana cewa hakkin ofishin ministan shari'a ne shi bada kariya da kuma shawara kan hakkin al'umma.

"Dole minista ya kula da hakkin 'yan kasa ba hakkin mutum daya tilo ba," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Abubakar Malami, SAN Facebook

Ana dai zargin gwamnatin Najeriya da kin mutunta hukuncin wasu kotuna da suka bayar da belin Sambo Dasuki da kuma Malam Zakzaky.

Amma Malami ya ce idan mutum daya ko biyo ko uku suka yi kokarin tayar da hankalin 'yan kasa wajibi ne a yi maganinsu ta hanyar daukar mataki na shari'a.

Ya kuma ce idan har aka sake ba shi jagorancin ma'aikatar shari'a yana son a dauki matakai na "ba sani ba sabo" kan duk wanda ya nemi kawo baraka ga hadin kan kasa.

"Mutum miliyan 180 suna da hakki na zaman lafiya da lumana."

"Gwamnati za ta ci gaba da bin mataki na tabbatar da abin da ta yi har sai an kai makura ta karshe," in ji shi.

An shafe makwanni mabiya Malam Ibrahim El-zazzaky na zanga-zangar neman a sako jagoransu, lamarin da ya kai su da yin artabu da jami'an tsaro inda har aka samu rasa rayuka da dama.

Labarai masu alaka