Lauyoyinmu na jiran takardar 'haramta' IMN domin nazari

Zakzaky
Image caption Mabiya SHeikh El-zakzaky sun ce sai inda karfinsu ya kare kan jagoransu

Mai magana da yawun kungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN, Ibrahim Musa ya ce kawo yanzu babu wani abu da za su ce illa dai jiran takardar 'haramta' ayyukan kungiyar ta same su.

Ibrahim Musa wanda ya shaida wa BBC hakan, ya ce lauyoyi da jagororin kungiyar na nazari kan abubuwan da takunsa domin fitar da matsaya.

Gwamnatin Najeriya ce dai ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement In Nigeria da na 'ta'addanci kuma haramtattu'.

Jaridar Punch Newspaper ce ta samu ganin wannan takardar inda ta ce ofishin ministan Shari'ar kasar ne ya nemi hukuncin a ranar Juma'a.

Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu ba bu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane ba yin kira kansu da suna 'yan Shi'a."

Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya.

"Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungiyar a kundin gwamnati da kuma manyan jaridun Najeriya guda biyu." In ji takardar.

Ci gaba da zanga-zangar da 'ya'yan kungiyar ke yi na neman a saki jagoransu da ke tsare a hannun gwamnati tun 2015, a Abuja da sauran sassan kasar na ci gaba da janyo asarar rayuka.

Ko a makon da ya gabata sai da 'yan sanda suka 'kashe' 'yan kungiyar 11 a Abuja a irin wannan zanga-zanga, inda su kuma 'yan sanda suka yi zargin 'yan kungiyar sun kashe babban jami'n 'yan sanda.

Ana sa ran cewa fadar gwamnati ko kuma ma'aikatar Shari'a ce za ta sanar da wannan hukuncin na 'haramta' ayyukan kungiyar ta IMN.

Idan har 'haramcin ya faru', to IMN za ta zama kungiya ta biyu bayan IPOB da Shugaba Muhammadu Buhari ya haramta a mulkinsa.

A shekarar 2017 ne gwamnatin Buhari ya haramta ayyukan kungiyar masu fafutukar neman ballewar yankin kudu maso gabas na Najeriya daga kasar wato IPOB.

To sai dai kungiyar IMN na da hurumin daukaka kara kasancewar ba su da wakilici lokacin da aka fitar da wannan hukunci.

Sharhi, Usman Minjibir

Wannan takarda dai na zuwa ne a ranar da tsohon ministan Shari'ar kasar, Abubakar Malami ya bayyana gaban majalisar dokokin kasar domin a sake tantance a matsayin minista a gwamnatin Buhari.

An tambayi tsohon ministan na shari'a dalilin da ya sa ya ki amincewa a saki tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Sambo Dasuki da kuma jagoran 'yan Shi'a a Najeriya Malam Ibrahim Zakzaky duk da kotu ta bayar da belinsu, sai ya ce hakkin ofishinsa ne ya kare hakkin 'yan Najeriya ba na wani mutum daya ba.

Ya ce Kundin mulki na Najeriya sashi na 174, ya bayyana cewa hakkin ofishin ministan shari'a ne shi bada kariya da kuma shawara kan hakkin al'umma.

"Dole minista ya kula da hakkin 'yan kasa ba hakkin mutum daya tilo ba," in ji shi.

Ana dai zargin gwamnatin Najeriya da kin mutunta hukuncin wasu kotuna da suka bayar da belin Sambo Dasuki da kuma Malam Zakzaky.

Amma Malami ya ce idan mutum daya ko biyo ko uku suka yi kokarin tayar da hankalin 'yan kasa wajibi ne a yi maganinsu ta hanyar daukar mataki na shari'a.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Har wa yau, ita wannan takarda na zuwa ne kwana uku kafin sake bayyanar shugaban kungiyar ta IMN, Sheikh Ibrahim Elzakzaky a kotu da ke zama a jihar Kaduna.

El-zakzaky da mai dakinsa dai na neman samun beli domin fita kasar waje neman lafiya kasancewar suna cikin 'matsanancin' hali na rashin lafiya.

Kotun dai ce ta dage sauraren bukatar neman belin a zamanta na ranar 18 ga watan Yuli har zuwa 29 ga watan na Yuli.

Tana iya yiwuwa gwamnati ta nemi a 'haramta' kungiyar ne domin yin amfani da hakan a gaban kotu.

Watakila kuma an samu hukuncin 'haramta' ayyukan kungiyar domin yin kandagarki na abin da zai je ya zo a ranar Litinin din, ranar da ake sa ran kotun ta Kaduna za ta yanke wannan hukunci.