Ban hana 'yan Shi'a yin shi'arsu ba - Buhari

Zakzaky
Image caption Tun shekarar 2015 ake tsare da Sheikh Ibrahim El-zakzaky

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce umarnin da kotu ta bayar na dakatar da kungiyar IMN bai hana mabiya Shi'a su gudanar da addininsu ba a kasar.

Kalaman shugaban na zuwa ne bayan hukuncin wata kotu a Abuja, ranar Juma'a, da ya bayar da umarnin haramta Kungiyar IMN ta mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky kamar yadda gwamnati ta nema.

Bayanan kotun sun nuna cewa gwamnati ta nemi a haramta kungiyar ta IMN bayan ayyana ta a matsayin ta 'yan ta'adda, inda ta zarge ta da haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya yi watsi da zargin cewa suna tayar da husuma, sannan ya shaida wa BBC lauyoyi da jagororinsu na nazari kan umarnin kotun domin fitar da matsaya.

Tashin hankali ya kazanta a baya-bayan nan tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan kungiyar, wadanda ke zanga-zanga akai-akai tun bayan tsare shugabansu da gwamnati ta yi a shekarar 2015.

Sai dai mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa za a aiwatar da wannan hukunci na kotu domin haramta kungiyar ta IMN, amma ya ce hakan ba yana nufin haramta Shi'a ba.

"Akwai miliyoyin 'yan Shi'a a kasar nan wadanda suke zaune lafiya kuma gwamnati ba ta da matsala da su, ba wanda zai tsangwama musu kaa yadda suke harkokinsu... Ba mu hana kowa yin Shi'arsa ba," in ji malam Garba.

Ya kara da cewa gwamnati ta nemi wannan hukunci ne domin "haramta ayyukan kungiyar IMN karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky".

Bayanan kotu

Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu babu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane da kiran kansu da suna 'yan Shi'a."

Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya.

"Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungiyar a kundin gwamnati da kuma manyan jaridun Najeriya guda biyu," in ji takardar.

Ci gaba da zanga-zangar da 'ya'yan kungiyar ke yi na neman a saki jagoransu da ke tsare a hannun gwamnati tun 2015, a Abuja da sauran sassan kasar na ci gaba da janyo asarar rayuka.

Ko a makon da ya gabata sai da 'yan sanda suka 'kashe' 'yan kungiyar 11 a Abuja a irin wannan zanga-zanga, inda su kuma 'yan sanda suka yi zargin 'yan kungiyar sun kashe babban jami'n 'yan sanda.

Ana sa ran cewa fadar gwamnati ko kuma ma'aikatar Shari'a ce za ta sanar da wannan hukuncin na 'haramta' ayyukan kungiyar ta IMN.

Idan har haramcin ya faru, to IMN za ta zama kungiya ta biyu bayan IPOB da Shugaba Muhammadu Buhari ya haramta a mulkinsa.

A shekarar 2017 ne gwamnatin Buhari ya haramta ayyukan kungiyar masu fafutukar neman ballewar yankin kudu maso gabas na Najeriya daga kasar wato IPOB.

To sai dai kungiyar IMN na da hurumin daukaka kara kasancewar ba su da wakilici lokacin da aka fitar da wannan hukunci.

Dalilin kin sakin Zakzaky

Wannan takarda dai na zuwa ne a ranar da tsohon ministan Shari'ar kasar, Abubakar Malami ya bayyana gaban majalisar dokokin kasar domin a sake tantance a matsayin minista a gwamnatin Buhari.

An tambayi tsohon ministan na shari'a dalilin da ya sa ya ki amincewa a saki tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Sambo Dasuki da kuma jagoran 'yan Shi'a a Najeriya Malam Ibrahim Zakzaky duk da kotu ta bayar da belinsu, sai ya ce hakkin ofishinsa ne ya kare hakkin 'yan Najeriya ba na wani mutum daya ba.

Ya ce Kundin mulki na Najeriya sashi na 174, ya bayyana cewa hakkin ofishin ministan shari'a ne shi bada kariya da kuma shawara kan hakkin al'umma.

"Dole minista ya kula da hakkin 'yan kasa ba hakkin mutum daya tilo ba," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Abubakar Malami ya shafe shekara uku da rabi a matsayin ministan Shari'a, kuma ana sa ran za a sake nada shi nan ba da jimawa ba

Ana dai zargin gwamnatin Najeriya da kin mutunta hukuncin wasu kotuna da suka bayar da belin Sambo Dasuki da kuma Malam Zakzaky.

Amma Malami ya ce idan mutum daya ko biyu ko uku suka yi kokarin tayar da hankalin 'yan kasa wajibi ne a yi maganinsu ta hanyar daukar mataki na shari'a.

Har wa yau, ita wannan takarda na zuwa ne kwana uku kafin sake bayyanar shugaban kungiyar ta IMN, Sheikh Ibrahim Elzakzaky a kotu da ke zama a jihar Kaduna.

El-zakzaky da mai dakinsa dai na neman samun beli domin fita kasar waje neman lafiya kasancewar suna cikin 'matsanancin' hali na rashin lafiya.

Kotun ce ta dage sauraren bukatar neman belin a zamanta na ranar 18 ga watan Yuli har zuwa 29.

Tana iya yiwuwa gwamnati ta nemi a haramta kungiyar ne domin yin amfani da hakan a gaban kotu.

Watakila kuma an samu hukuncin haramta ayyukan kungiyar domin yin kandagarki na abin da zai je ya zo a ranar Litinin din, ranar da ake sa ran kotun ta Kaduna za ta yanke wannan hukunci.

Labarai masu alaka