Sudan na neman kara rincabewa

Sudan
Image caption An zargi jami'an tsaron Sudan da yin amfani da karfi fiye da kima

An harbe masu zanga-zanga biyar a garin Kordofan da ke arewacin Sudan, a yayin wani gangami da aka yi a ranar litinin, kamar yadda wani kwamitin likitoci masu alaka da zanga-zangar ya bayyana.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, a kalla mutum biyu da aka harbe dai 'yan makarantar sakandare ne wadanda suka fito zanga-zanga a kan titunan birnin El Obeid.

Tun watan disamban da ya gabata ne dai ake ta fama da zanga-zangar kin jinin gwamnati a Sudan, lamarin da ya janyo aka hambarar da shugaban kasar Omar Al-Bashir, a watan Afrilun da ya gabata.

A ranar Asabar din da ta gabata, ofishin mai shigar da kara ya ce za a tuhumi a kalla jami'an soji takwas da laifukkan keta hakkin dan adam bayan da suka kashe masu zanga-zanga 87.

Likitoci da suke da alaka da 'yan adawa dai sun ce mutum 130 ne suka rasa rayukkansu, bayan da jami'an tsaron suka bude wuta kan masu zanga-zanga a ranar uku ga watan Yuni.

Labarai masu alaka