Sarkin Dubai zai gurfanar da matarsa gaban kotu

Gimbiya Haya ta tsere wa mijin nata daga Dubai inda yanzu take zaune a Landan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gimbiya Haya ta tsere wa mijin nata daga Dubai inda yanzu take zaune a Landan

A ranar Talatar nan ne daya daga cikin manyan hamshakan shugabanni masu arziki da matsayi a Gabas ta Tsakiya zai kai karar matarsa da suka samu sabani, gaban wata kotu a Landan.

A shari'ar wadda ta dauki hankalin duniya, Sheikh Mohammed Al-Maktoum, mai shekara 69, da ke mulkin Dubai zai kai karar Gimbiya Haya a kan batun kula da 'ya'yansu.

Gimbiya Haya mai shekara 45, wadda 'yar uwar sarkin Jordan ce, ta tsere daga Dubai zuwa Landan a farkon shekarar nan, kuma abokananta sun ce tana cikin fargaba game da rayuwarta.

Shugabannin kasashen Larabawa na yankin Fasha galibi suna daga cikin mutanen da a duniya suke tafiyar da harkokinsu na rayuwa cikin sirri, to amma wannan shari'ar tuni ta dauki hankalin duniya.

Sarkin na Dubai wanda yana daya daga cikin hamshakan masu hannu a gasar sukuwar dawakai ta duniya, yana da dukiyar da ta kai ta sama da fam biliyan uku.

An ruwaito cewa ya rubuta wata waka ta bacin rai wadda a ciki yake zargin wata mata da bai ambaci sunanta ba da cin amana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana ganin Gimbiya Haya wadda ta yi makaranta a Dorset da Oxford tana son zama ne a Birtaniya

Da farko Gimbiya Haya ta gudu Jamus a shekarar nan inda ta nemi mafaka. Daga baya kuma ta tafi Landan, inda yanzu aka ce tana zaune a wani gida da kudinsa ya kai dala miliyan 107 aKensington Palace Gardens, a tsakiyar Landan.

Wata shakikiyar Gimbiyar ta bayyana cewa, a kwanan nan ta gano wani zargi da ake yi na tilasta mayar da daya daga cikin 'ya'yan Sarkin mata, zuwa Dubai, a shekarar da ta wuce.

Yarinyar ta uku daga cikin 'ya'yan gidan sarautar Sheikh Mohammed, ta tsere a 2001, kuma ana zargin an sace ta a Cambridge aka mayar da ita Dubai.

Rahotanni sun ce Sheikh Mohammed yana da 'ya'ya 23 da ya haifa da mata daban-daban.

Ana ganin Jordan ba za ta ji dadin wannan shari'a ba, saboda Gimbiya Haya kanwar Sarki Abdullah na Jordan ce, kuma akwai 'yan Jordan kusan dubu 250 da ke aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa, suke tura kudade gida, wanda a kan hakan Jordan ba za ta so ta samu sabani da Dubai ba.

Labarai masu alaka