Wasunmu ko sallah ba sa yi – tsohon dan Boko Haram

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matasa da dama ne suka shiga kungiyar ta Boko Haram, saboda dalilai da dama

A yayin da aka cika shekara 10 da fara rikicin kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, wani tsohon dan kungiyar ya bayyana wa BBC cewa wasu mambobin kungiyarsu ba sa yin sallah.

Matashin wanda da ya ce ya tuba daga kasancewa dan kungiyar, ya ce da farko rashin aikin yi ne ya ja hankalinsa har ya shiga kungiyar.

Kungiyar ta ja hankulan dubban matasa domin shiga cikinta, yayin da ta tilasta wa wasu dubban ta hanyar sacewa da yi musu barazanar kisa matukar suka yi kokarin ficewa.

Ya ce bayan ya shiga ya dauka cewa duk abin da yake yi yana yi ne da sunan addinin Musulunci, kafin daga baya ya gano gaskiyar lamari.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Saurari hirar da muka yi da tsohon dan Boko Haram

"Lokacin da suka yaudare mu muka shiga wannan abin, sun yaudare mu bisa kamar Musulunci. Kuma da muka duba muka gani sai muka ga ba musulunci ba ne, illa dai yaudara." A cewar matashin da ya tuba daga Boko Haram, wanda bai so a ambaci sunansa ba.

Yace tun da farko rashin aikin yi ne ya sa su suka shiga kungiyar. Ya ce a lokacin da suka shiga sun ga wani abokinsu yana zuwa da kudi, yayin da su kuma suke fafutukar neman aikin da za su rinka yi suna samun kudi.

Ya kara da cewa abokin nasu ya fara jan wasu daga cikinsu, inda a farko ake biyan su naira 3,000 a duk lokacin da suka kai hari, ko suka kwato kudi ko kuma aka biya su kudin fansa.

A cewar matashin dai, tun suna zaune a cikin gari ayyukan da suka fara yi shi ne yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Daga baya kuma ya ce sun koma daji inda ake tura su leken asiri, da kuma tattara bayanai a wajen da ake so a kai hari.

Ya ce a lokacin abin da ake ba su bai wuce naira dubu uku ba. "Kuma za a ce akwai manya wadanda za su zo su ba su naira 500,000 ko naira 600,000.

Sai dai ya ce har ya fita daga kungiyar bai taba ganin wani babba a kungiyar ba, in dai ba wasu da za su zo da manyan bindigogi su ba su ba a wasu lokutan.

Ya ce daga baya sun fita sun bi su cikin jeji inda aka fara tsangwamar su da kuma takura.

Hakkin mallakar hoto AUDU MARTE
Image caption Boko Haram na yawan kai wa masu jana'iza hari

Matashin wanda ya shafe shekara takwas tare da Boko Haram, ya ce da farko yana jin dadin cewa addinin musulunci yake yi wa aiki.

Amma daga baya da ya gano cewa kungiyar ta kauce wa addinin musulunci ya shiga damuwa sosai.

"Ga Kur'ani a ajiye…da na duba na gani Allah ya hana zina, ya hana shaye-shaye, sai na ga cewa ga kwayoyin, ga zinar, a kamo mata a zo a yi ta zina da su, wani ma bai damu da sallah ba kuma za a zo a kashe wanda yake sallar." A cewar matashin.

Ya ce shi ya sa suke yanke hukuncin cewa ba don Allah ake wannan abin ba. Kuma suka yanke shawarar fita daga kungiyar.

Ya ce kungiyar tana tura mutane kasuwanni da kauyuka domin leken asiri da tattara bayanai, da kuma nazartar yanda yanayin tsaro yake a kasuwar.

Ya kara da cewa su ne suke ba da shawara a lokacin cewa ko za a shiga a kai hari, ko kuma suce kada a je idan sun ga akwai jami'an tsaro da dama.

Matashin yace babban abinda yake nadama a kasancewar sa dan Boko Haram shi ne kashe wani tsoho da ya yi yayin da suka kai hari a kauyen Gajaganna.

Ya ce bisa kusukere ya harbi tsohon, kasancewar a lokacin bai iya rike bindiga ba.

Ya ce duk lokacin da ya tuna hankalinsa yana tashi, kuma a wasu lokutan idan ya rufe ido sai ya ringa ganin tamkar tsohon yake dawo masa.

A kimanin shekara takwas da ya shafe tare da 'yan Boko Haram ya ce bai taba ganin shugaban kungiyar Abubakar Shekau ba, ko wasu manyan na kusa da shi.

Ya ce da dama daga cikinsu sun ringa fatan yin arba da Shekau din su kashe shi, saboda irin zaluncin da yace ake yi musu.

A cikin dajin dai ba a basu kudi, kuma ba a barinsu su shiga gari, sai dai idan za a tura su leken asiri.

Idan manyan su za su fita gari, ana tambyar su ko akwai abinda suke so a sayo musu, amma dai ba a ba su kudi.

Daga karshe matashin tare da wasu takwarorinsa su kimanin 20 sun yanke hukuncin barin kungiyar, bayan da suka gaji da kuncin rayuwa da suke fuskanta.

Kuma tsakar dare suka bar sansanin na Boko Haram yayin da shugabannin suke barci.

Sun mika kansu ga sojojin Najeriya, inda bayan yi musu tambayoyi aka koyar da su sana'o'i.

A yanzu matashin ya koyi sana'ar kafinta, kuma yace rayuwarsa ta inganta, domin yana yin aiki ana biyansa, kuma yana samun karbuwa a sana'ar ta sa.

Labarai masu alaka