Pakistan: Jirgin sojoji ya yi hatsari a kan gidajen mutane

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Pakistan military plane crash reduces buildings to rubble

A kalla mutum 18 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata yayin da wani karamin jirgin soji ya yi hatsari a wata unguwa da ke kusa da birnin Rawalpindi na Pakistan

Mutum biyar da ke cikin jirgin da kuma fararen hula 13 na daga cikin wadanda suka muu a cewar hukumar agaji.

Jirgin yana gudanar da atisaye ne lokacin da ya yi hatsarin, sai kuma wuta ta tashi a gidaje da dama da ke yankin. Wani ganau ya cejirgin ya kama da wuta kafin ya yi hatsarin.

Rahotanni sun ce jirgin samfurin King Air 350 ya yi wata juyawa ne a lokacin da yake daf da inda zai sauka, kafin daga bisani ya fado.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hedikwatar rundunar sojin kasar na birnin Rawalpindi ne

Rawalpindi, wacce ke kusa da babban birnin kasar Islamabad, can ne inda hedikwatar rundunar sojin Pakistan take, kuma jirgin mallakin sojin saman Pakistan ne.

Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya mika sakon ta'aziyarsa da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, kamar yadda gwamnatin kasar ta wallafa a Twitter.

Ta yaya jirgin ya fado?

Ganau da suke wajen sun ce jirgin ya yi hatsarin ne inda ya fada wani gida a unguwar da misalin karfe 7.00 na safe agogon GMT.

''Idona biyu a lokacin da na ji jirgin na wucewa ta saman gidana kuma yana cin wuta,'' a cewar wani mazaunin unguwar Ghulam Khan.

''Karar na da ban tsoro, karamin jirgi ne. Daga nan sai ya fada kan wani gida da wasu iyalai ke zama.''

Wani ganau din kuma Yasir Baloch, ya ce: "Jelar jirgin na ci da wuta kuma bai fi dakika biyu zuwa uku ba sai ya fado nkan gidajen mutane gaba kadan da gidana ya kone kurmus.

Wani mazaunin wajen da abin ya faru wanda ya ce sunansa Yamin ya ce ya samu tserewa daga gidansa da ya kama da wuta shi da matarsa da 'yarsa da kuma iyayensa, amma dan uwansa da matarsa da dansu sun mutu.

''Taga da kofar dakinsu sun kasance a kulle. Mun yi iya bakin kokarinmu mu bude musu su fito amma hakan bai yiwuwa ba,'' in ji shi.

Hotunan da aka dauka na wajen da abin ya faru sun nuna yadda gidaje suka yi baki saboda konewa da kuma baraguzai.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na FP ya ce hayaki ya dade yana tashi daga gidajen da suka kone.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane sun taru a wajen da abin ya faru suna jimami

Hukumar bayar da agaji ta ce tuni aka garzaya da wadanda suka ji rauni asibiti, sannan kuma an kwashe gawarwakin wadanda suka mutu don a gane ko su waye.

Mai magana da yawun hukumar Farooq Butt, ya ce ''gawarwakin sun kone sosai, dole sai an yi gwajin kwayoyin halitta don a agne su.''

Sau nawa ana samun irin haka a Pakistan?

An sha samun haduran jirgi a Pakistan.

A shekarar 2010, wani jirgin kamfanin Airblue ya yi hatsari a kusa da Islamabad, inda mutum 152 da ke ciki suka mutu - hatsarin jirgi mafi muni a tarihin Pakistan.

A 2012 kuma jirgi samfurin Boeing 737-200 na kafanin Bhoja Air ya yi hatsari saboda rashin kyawun yanayi a yayin da ya kusa sauka a Rawalpindi, inda duk mutum 121 da ke ciki suka mutu.

A 2016 kuma wani jirgin mai zirga-zirga a kasashen duniya ya yi hatsari yayin da ya taso daga arewacin Pakistan zuwa Islamabad, kuma mutum 47 suka mutu.

Labarai masu alaka