Ana gudanar da sabuwar zaga-zanga a Sudan

Sudan
Image caption Kashe dalibai na neman janyo sabuwar zanga-zanga a Sudan

Wakilan BBC a Sudan sun bayyana cewa wasu masu zanga-zanga sun taru domin nuna fushinsu a birane da suka hada da babban birnin kasar wato Khartoum.

Hakan na zuwa ne bayan da aka kashe masu zanga-zangar biyar a garin Kordofan da ke Arewacin kasar.

A kalla hudu dai daga cikin wadanda aka kashe yara 'yan sakandare ne.

Kungiyar Kwararru ta The Sudan Professional's Association wadda ta jagoranci yawancin zanga-zangar da ake ta fama a duk fadin kasar na tsawon watanni, al'amarin da ya janyo saukar shugaban kasar Omar-al Bashir, ta ce gwamnati mai mulki ta soji ya kamata a daura wa alhakin kashe-kashen nan.

Ta kuma yi kira ga mutanen duk fadin kasar da su fito su ci gaba da gudanar da zanga-zangar. Sannan ta bukaci da a mika wa fararen hulla mulkin kasar cikin gaggawa.

Harbe yara hudu da kuma babba guda daya da aka yi a yayin wata zanga-zangar da aka yi a garin Kordofan da ke Arewacin kasar a ranar Litinin na cikin yunkurin da ake yi na samar da gwamnati ta farar hula a kasar, kamar yadda wani mamban kungiyar ya shedawa BBC.

Wani fefen bidiyon da aka samu daga birnin El Obeid da ke Arewacin Kordofan na nuna yadda aka dinga harbe dalibai cikin kayan makarantarsu a lokacin da suka yi wani tattaki da niyyar bayyana bukatunsu na samar da yanayin rayuwa ingantace, a cewar wakilinmu.

A cikin wani bidiyon kuma, an nuna yadda wani jami'in soji ya afkawa masu zanga-zangar tare da kuma bude musu wuta.

Hotunan wani asibiti na daban su ma sun nuna mutane jina-jina a kwance.

A cewar kwamitin likitocin Sudan, wanda ke da alaka da zanga-zangar, ya ce mutum 62 ne suka samu raunuka a birnin El-Obeid.

Tuni dai jami'an gwamnati suka sanar da dokar ta bacci a kan yankin da lamarin ya faru, tare da sanya dokar hana zirga-zirga.

Labarai masu alaka