Shin da gaske ne Annabi Isa ya bayyana a Kenya?

Jesus Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Mutane da dama na kwaikwayon Isa Almasihu

Wasu hotuna da fefen bidiyo da aka yada sosai a kafafen sada zumunta a Afirka sun nuna yadda wani mutumi ya yi shiga irin ta Isa Almasihu.

Abin tambaya shi ne wane ne wannan mutumin kuma mai yake yi?

Daya daga cikin sakonnin da aka wallafa a kansa, mutane kusan so 8,000, suka far wa sakon ciki har da wani dan siyasar adawa na kasar Afirka ta kudu Julius Malema, inda ya ce ''wani fasto daga kasar Afirka ta kudu ya gayyaci annabi Isa daga sama domin ya yi wa'azi a cocinsa''.

Mutumin dai wani dan Amurka ne mai wa'azi da kuma wasan fina-finai mai suna Michael Job, wanda ke halartar tarurukan adinin kirista a matsayin babban bako.

Michael dai na zaune a birnin Orlando da ke Florida, inda ya jima yana fitowa kamar Isa almasihu a wasanni da ake yi a filin wasan The Holy Land Experience, wanda aka dauka kamar gidan tarihi.

A cikin wani bidiyon da ya wallafa a kan shafinsa na Facebook, a makon da ya gabata, za a iya ganin shagunan kujeru da kuma filayen noma a Kenya kamar yadda aka gani a hoton da ya ce ya dauka a Afirka ta kudu.

Masu amfani da shafin Twitter dai sun mayar da hotunan nasa abin dariya da kuma yadda ya ke yi wa mutane alkawuran canza rayyukansu.

An saka daya daga cikin hotunan nasa a kan wani shafin intanet, inda suka ce ''wani faston kasar Kenyan ya yi ikirarin cewa ya tsinci Isa almasihu yana tafiya a kan titunan Kenya''.

Wata mai suna Adaakokwa kenan take dariyar lamarin nasa kan shafin Twitter.

A daya daga cikin bidiyon wa'azin da ya yi a Kenya, mai wa'azin wanda ya fito daga kasar Amurka ya yi alkawuran bai wa mutane lafiya tare da kuma gyara rayyukansu - lamarin da ya janyo masa suka kan shafukkan sada zumunta.

Wannan dai ba shi ne karonsa na farko da ya kawo wa Afirka ziyara ba, ko da a farkon wannan shekarar ya ziyarci kasar Togo, duk da cewa hotunansa da aka wallafa a lokacin sun nuna shi sanye da riga da wando maimakon shigar Isa almasihu da ya yi a Kenya.

Labarai masu alaka