Yadda sojoji ke 'kama' masu dada a Najeriya

A

An zarge sojojin Najeriya da kama maza masu kitso da kuma gashi mai launi a garin Aba da ke kudu maso gabashin kasar.

''Sojojin wadanda suka rufe fuskokinsu suna dukan duk wanda suka kama tare da amfani da almakashi wajen yanke musu gashi."

"Daga baya sai su jefa su a cikin motocinsu kuma su tafi da su,'' kamar yadda wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa jaridar Punch.

Bayan hakan a kan kai mazan wani wurin da ba a san ko ina ne ba.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Majo Aliu Kadiri ya fada wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa sun san da lamarin kuma suna iya kokarinsu wajen ganin sun gano gaskiyar al'amarin.

Sai dai ba a san ko lamarin yana da alaka da shirye-shiryen da jami'an tsaro ke gudanarwa a kasar na kokarin kawar da satar mutane ba.

Har ila yau rundunar sojin kasar suna gudanar da wani shiri domin kawar da masu satar shanu da kuma kawo karshen 'yan ta'adda da ake fama da su a arewa maso gabashin kasar.

Wannan ba shi ne karo na farko da jami'an tsaron Najeriya su ke mayar da hankali kan maza masu dada ba.

A cikin watan Maris da ya gabata, wasu sanda da ke kula da dakile gungun masu laifi sun harbe wani mutum a wata unguwar da ke da yawan hada-hada, bayan da suka yi kokarin kama wani mutum mai kitso a cikin wani wurin shakatawa.

A lokacin wani mai magana da yawun 'yan sanda ya gayyawa sashen Pidgin na BBC cewa an fi mayar da hankali kan kama maza masu kitso da kuma zane a jiki.

Labarai masu alaka