Shi'a: Haramta IMN tamkar take musu hakkin addini ne - HRW

Zakzaky
Image caption Sheikh El-zakzaky na tsare a hannun gwamnati tun 2015

Kungiyar Kare Hakkin Dan'adam ta Human Rights Watch ta ce haramta kungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN take hakkin damar yin addini ne ga yan Najeriya.

A wata sanarwa da HRW ta fitar, Enietie Ewang wadda ita ce mai bincike ga kungiyar, ta ce " Ya kamata gwamnati ta warware haramcin da ta sanya wa kungiyar wanda ya hana 'ya'yan 'yancin haduwa ba tare da yamusti ba."

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement In Nigeria da na 'ta'addanci kuma haramtattu'.

Jaridar Punch Newspaper ce ta samu ganin wannan takardar inda ta ce ofishin ministan Shari'ar kasar ne ya nemi hukuncin.

Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu ba bu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane ba yin kira kansu da suna 'yan Shi'a."

Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya.

"Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungiyar a kundin gwamnati da kuma manyan jaridun Najeriya guda biyu." In ji takardar.

Ci gaba da zanga-zangar da 'ya'yan kungiyar ke yi na neman a saki jagoransu da ke tsare a hannun gwamnati tun 2015, a Abuja da sauran sassan kasar na ci gaba da janyo asarar rayuka.

Ko a makon da ya gabata sai da 'yan sanda suka 'kashe' 'yan kungiyar 11 a Abuja a irin wannan zanga-zanga, inda su kuma 'yan sanda suka yi zargin 'yan kungiyar sun kashe babban jami'n 'yan sanda.

Ana sa ran cewa fadar gwamnati ko kuma ma'aikatar Shari'a ce za ta sanar da wannan hukuncin na 'haramta' ayyukan kungiyar ta IMN.

Idan har 'haramcin ya faru', to IMN za ta zama kungiya ta biyu bayan IPOB da Shugaba Muhammadu Buhari ya haramta a mulkinsa.

A shekarar 2017 ne gwamnatin Buhari ya haramta ayyukan kungiyar masu fafutukar neman ballewar yankin kudu maso gabas na Najeriya daga kasar wato IPOB.

To sai dai kungiyar IMN na da hurumin daukaka kara kasancewar ba su da wakilici lokacin da aka fitar da wannan hukunci.

Labarai masu alaka