Duk mabiyin El- Zakzaky dan ta'adda ne - 'Yan sanda

Zakzaky
Image caption Sheikh El-zakzaky na tsare a hannun gwamnati tun 2015

Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce daga yanzu za su dauki duk wani dan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da aka fi sani da 'yan Shi'a a matsayin dan ta'adda bisa la'akari da hukuncin babbar kotu da gwamnati ta samu.

Sifeto Janar wanda ya bayyana hakan a hedikwatar 'yan sandan da ke Abuja a yayin wani taron manyan 'yan sanda na wata-wata ranar Talata, ya ce ayyukan kungiyar da yunkurin jefa Najeriya rikicin kabilanci.

Mohammed Adamu ya yi karin haske dangane da mambobin kungiyar IMN 63 da suka hada da mata bakwai wadanda ke hannun 'yan sandan, inda ya ce daga yanzu duk dan kungiyar ta IMN da suka kama to za su gurfanar da shi ne a gaban kotu domin fuskantar hukunci irin na ta'addanci.

Ya kara da cewa " ayyukan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da Sheikh Zakzaky ke jagoranta sun dade suna barazana ga tsaro da doka da oda na Najeirya da kuma zaman lafiya da jogaranci na gari da ma kimar tarayyar Najeriya na kasa mai cin gashin kai."

Sifeto Janar din ya kuma kawo wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar da ya ce sun yi karo da ayyukan kungiyar .

Ya ci gaba da cewa " saboda haka daga yanzu duk wani mutum ko ya alakanta kansa da ayyukan kungiyar ta kowace hanya, da za su iya tallafa wa IMN to dole a hukunta a matsayin dan ta'adda, makiyin kasa sannan kuma mai yi wa Najeriya zagon kasa. Ma'anar hakan ita ce duk wani nau'i na zanga-zanga da IMN take yi sun haramta kuma ya saba doka."

To sai dai sifeton na 'yan sanda ya yi karin haske cewa " a dai-dai lokacin da duk wani mabiyin mazhabar Shi'a yake da damar yin akidarsa ba tare da tsangwama ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su, kungiyar Elzakzaky ta Islamic Movement of Nigeria wadda ba ta yadda da kundin tsarin mulki ba da gwamnatin Najeriya, ita kadai ce kungiyar da aka haramta aka kuma bayyana ta da kungiyar 'yan ta'adda."

Hakkin mallakar hoto SODIQ ADELAKUN
Image caption An sha samun taho mu-gama tsakanin 'yan sanda da 'yan Shi'a

Takardar da ta haramta IMN

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement In Nigeria da na 'ta'addanci kuma haramtattu'.

Jaridar Punch Newspaper ce ta samu ganin wannan takardar inda ta ce ofishin ministan Shari'ar kasar ne ya nemi hukuncin.

Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu ba bu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane ba yin kira kansu da suna 'yan Shi'a."

Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya.

"Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungiyar a kundin gwamnati da kuma manyan jaridun Najeriya guda biyu." In ji takardar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ci gaba da zanga-zangar da 'ya'yan kungiyar ke yi na neman a saki jagoransu da ke tsare a hannun gwamnati tun 2015, a Abuja da sauran sassan kasar na ci gaba da janyo asarar rayuka.

Ko a makon da ya gabata sai da 'yan sanda suka 'kashe' 'yan kungiyar 11 a Abuja a irin wannan zanga-zanga, inda su kuma 'yan sanda suka yi zargin 'yan kungiyar sun kashe babban jami'n 'yan sanda.

Yanzu haka kungiyar IMN ta zama kungiya ta biyu bayan IPOB da Shugaba Muhammadu Buhari ya haramta a mulkinsa.

A shekarar 2017 ne gwamnatin Buhari ya haramta ayyukan kungiyar masu fafutukar neman ballewar yankin kudu maso gabas na Najeriya daga kasar wato IPOB.

Mene ne martanin IMN?

Har kawo yanzu kungiyar IMN ba ta ce komai ba dangane da umarnin da sifeton 'yan sadan ya bai wa 'yan sanda a ranar Talata.

Sai dai a baya kungiyar ta IMN ta bakin mai magana da yawunta, Ibrahim Musa ya shaida wa BBC cewa "haramta IMN wani yunkuri ne na gwamnati na kawar da hankalin jama'a daga irin musgunawar da gwamnati ke yi wa 'yan kungiyar."

Ya kara da cewa "ba za mu fasa bin hanyoyin da muka saba bi ba na neman hakkokinmu."

Ibrahim Musa ya kuma ce "idan ana so mu daina tattaki a Abuja to a saki jagoranmu, Malam Ibrahim Elzakzaky."

Ra'ayin lauyoyi kan 'haramta' IMN

Batun haramta kungiyar IMN na daga cikin batutuwan da ya raba kan lauyoyi dangane da dacewa ko akasin haka da kuma yiwuwar warware haramcin.

Barrister Audu Bulama Bukarti lauya dan Najeriya mazaunin birnin London, ya shaida wa BBC ranar Litinin cewa "'yan kungiyar IMN za su komawa kotun da ta bayar da hukuncin haramci a kanta kasancewar da ma tun asali kungiyar ba ta samu wakilci ba a kotun."

Dangane kuma da ko jami'an tsaro za su iya amfani da karfi a kan 'yan kungiyar kasancewar kotu ta bayyana su da 'yan ta'adda, sai barrister Bulama ya ce "doka ce kawai za ta iya tabbatar da haka saboda haka jami'an tsaro za su kama 'yan kungiyar ne su gurfanar da su gaban kotu domin hukunci."

Yadda haramta IMN ya raba kan 'yan Najeriya

Kamar yadda wannan batu ya raba kan lauyoyi, haka ma kan 'yan Najeriya ya rabu dangane da cancanta ko rashin cancantar haramtawar.

Tuni dai kungiyoyin kudancin kasar irin da dama suka yi Allah-wadai da haramta kungiyar, inda kuma na arewa da dama suka yi san barka da batun haramcin.

kungiyoyin masu rajin kare hakkin dan adam a ciki da waje su ma sun ga beken matakin gwamnati kan hukuncin da ta dauka ga IMN.

Ko a ranar Talatar nan ma sai da kungiyar kare hakkin bil'adama ta duniya, Human Rights Watch, HRW ta ce "haramta IMN tamkar dakile wa 'yan kungiyar 'yancin walwalar addini ne," inda ta nemi gwamnati da ta sake tunani.

Labarai masu alaka