Barazanar Ebola ta karu a Congo

Reuters Hakkin mallakar hoto Reuters

An kara samun bullar cutar Ebola karo na biyu a garin Goma da ke Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo. Garin Goma dai gari ne da ke da iyaka da kasar Rwanda wanda tuni aka tsaurara matakai a kan iyakar kasashen biyu domin dakile yaduwar cutar.

Wannan ne karo na biyu da ake samun bullar cutar Ebola bayan barkewarta a karo na biyu a fadin kasar.

An bayyana cewa mara lafiyar da ya kamu da cutar ta Ebola, ya shiga garin na Goma ne kusan makonni biyu da suka gabata, amma sai a makon jiya ne alamomin cutar suka fara nunawa a tattare da shi.

Tuni dai aka kebe shi inda aka ajiye shi a wata sabuwar cibiyar kula da wadanda suka kamu da cutar ta Ebola, domin lura da kuma duba lafiyarsa.

Kwararru da likitoci na ci gaba da bin diddiki domin gano wadanda ake zargi mara lafiyar ya yi mu'amala da su a 'yan kwanakin da suka gabata domin ba su riga kafin cutar.

Wannan ne dai karo na biyu da ake samun bullar cutar a garin na Goma, sai dai babu tabbacin wanda ya kamu da cutar a farko da kuma na biyu ko suna da wata alaka ko dangantaka.

Kasar ta Congo wadda ke yankin tsakiyar Afrika, na fuskantar mummunar barazanar cutar ta Ebola inda daga bara zuwa yanzu, sama da mutane 1,700 ne suka rasa rayukansu.

Ko a makon da ya gabata sai da Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce ba za ta bai wa 'yan kasar ta Congo izinin shiga kasarta don yin aikin hajji ba.

Inda a cewar ma'aikatar, an dakatar da bai wa 'yan kasar ta Congo biza domin a kare sauran mahajjata daga kamuwa da annobar.