Shin Koriya ta Arewa na shirin yaki ne?

AFP Hakkin mallakar hoto AFP

Rundunar sojin Korea ta Kudu ta bayyana cewa Korea ta Arewa ta harba wasu makamai masu linzami biyu da ke cin gajeren zango, inda ta ke zargin ta harbo su ne daga gabar tekun kasar ta gabas.

Wannan shi ne karo na biyu da kasar ke harba irin wadannan makamai cikin 'yan kwanakin nan inda ta harba wasu makaman biyu a cikin tekun Japan a Larabar da ta gabata.

Ministan tsaron Korea ta Kudu ya bayyana cewa wadannan makaman da Korea ta Arewa ta harba a wannan karon, sun sha bam-bam da wadanda ta harba a makon da ya gabata.

Ya ce makamai masu linzamin da kasar ta harba da ke cin kajeren zango sun nufi arewa maso gabas inda suka shafe tafiyar kusan kilometer 250 kafin suka sauka a cikin tekun Japan.

Koriya ta Arewa, ta bayyana makaman da ta harba a makon da ya gabata a matsayin gwaji kuma a matsayin gargadi ga Koriya ta Kudu ganin cewa Koriya ta Kudun na shirin wani atisayen hadin guiwa da Amurka a watan gobe.

Sai dai Amurka ta yi watsi da wannan gwajin da Koriya ta Arewar ta ce take yi, inda Shugaba Trump na Amurkar ya bayyana cewa, kasashe da dama suna gwajin makamai masu linzami da ke cin gajeren zango.

Haka kuma rahotanni sun ce Mista Trump din ya aikawa Shugaban Koriya ta Arewa Kim-Jong-un hotunansu a ganawar da suka yi a iyakar koriyoyin biyu a watan Yuni.

Wani jami'in fadar gwamnatin Amurka ya bayyana cewa yana sa ran nan da 'yan kwanaki kadan za a fara wata tattaunawa tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

Labarai masu alaka