Ronaldo ya harzuka magoya baya

Masu sha'awar wasan Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan kallon har kira da yaba wa abokin hamayyarsa Lionel Messi suka rika yi

Masu sha'awar kwallon kafa da ke cike da takaicin kin wasan da Cristiano Ronaldo ya yi a karawar sada zumunta da Juventus ta yi a Koriya ta Kudu sun harzuka suna neman diyya.

An tsara cewa gwarzon dan wasan zai taka leda tsawon minti 45 a karawar ta Juventus da kungiyar Koriyar ta K League All Stars, in ji wadanda suka shirya wasan amma sai Ronaldon ya zauna a benci kawai.

Masu sha'awar dan wasan sun harzuka da suka ga ba shi da alamar shiga wasan, inda suka rika kiran sunan abokin hamayyarsa Lionel Messi suna yabonsa.

Wasu daga cikin 'yan kallon a yanzu sun tunkari wani kamfanin lauyoyi a birnin Seoul, mai suna Myungan domin shigar da kara kan kin biya musu bukatarsu da Ronaldon ya yi ta shiga wasan.

Suna neman a biya su diyya ta makudan kudade kan tikitin da suka saya da kamashon da aka samu na sayar da tikitin da kuma diyya kan bata musu rai da lamarin ya yi.

Wani lauya ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa a ka'ida za a mayar wa wadanda suka shigar da karar kudin tikitinsu ne, to amma a wannan, lamarin na daban ne, saboda kamfanin da ya shirya wasan ya yaudari masu sha'awar wasan Ronaldon, ta hanyar sanarwar karya.

Lauyan ya ce a lokacin hirar da Reuters ya samu mutum biyu da suka gabatar da bukatarsu ta neman shigar da kara, amma kuma yana ta samun kira ta waya, wanda yana ganin masu bukatar za su kai kusan dubu 60.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Duk tsawon lokacin wasan Ronaldo yana kan beci

Robin Chang shugabar kamfanin Fasta na kasar ta Koriya ta Kudu, da ya shirya wasan, ta fashe da kuka a lokacin da ake tattaunawa kan batun da ita a gidan rediyo na SBS, kuma ta tabbatar cewa a ka'ida an shirya cewa gwarzon dan wasan na Portugal zai taka leda tsawon minti 45.

To amma Ms Chang ta ce sai da aka dawo hutun rabin lokaci minti 10 da wasa ta san cewa dan wasan mai shekara 34 ba zai shiga ba.

Ta ce lokacin da ta tunkari mataimakin shugaban kungiyar Juventus Pavel Nedved da maganar, sai ya gaya mata cewa shi ma da son samunsa ne da Ronaldon zai shiga, amma ya ce mata dan wasan ba ya so ya shiga, saboda haka ba abin da zai iya yi a kai, ta ce hakan ya bata mata rai matuka.

Hukumar kula da wasan kwallon kafar kwararru ta Koriya ta Kudu, K League, ta ce an aika wa Juventus takardar korafi kan saba wa yarjejeniyar wasan.

Mutane da dama masu sha'awar wasan suna ta bayyana bacin ransu a kan Ronaldo a shafukan intanet.

Wani wanda ya je kallon wasan ya rubuta a Instagram cewa ya ci amanar 'yan kallo dubu 60, kuma ya wulakanta mu.

''Na dawo daga rakiyarsa.''