Amnesty International ta gargadi Buhari kan haramta IMN

IMN Hakkin mallakar hoto SODIQ ADELAKUN
Image caption 'Yan Shi'a na kungiyar IMN na zanga-zangar neman a saki jagoransu

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta ce ta damu hakika dangane da yadda hukumomin Najeriya ke ci gaba da tauye wa 'yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria hakkinsu na walwalar addini da haduwa wuri guda.

A wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na twitter, Amnesty International ta ce "haramta IMN wani yunkuri ne na dauke hankalin jama'a daga batutuwan da suka jibanci kungiyar kamar neman hakkin jinin mutum 349 da sojoji suka kashe a Zaria a watan Disamban 2015 da na sauran magoya bayan IMN da jami'an tsaro suka kashe a 'yan shekarun nan."

Kungiyar ta Amnesty ta kara da cewa "'yan kungiyar ta IMN da dama sun yi batan dabo tun 2015 inda 'yan uwansu ba su san halin da suke ciki ba kuma gwamnati na nuna halin ko-in-kula wajen bin hakkin mutanen."

Sanarwar ta kuma ce duk da kin bin umarnin da babbar kotun Abuja ta bayar a watan Disamban 2016 na a saki shugaban IMN, Sheikh Ibraheem Elzakzaky da gwamnati ta yi, ana kuma ci gaba da jan kafa wajen bayar da belinsa duk kuwa da irin rashin lafiyar da yake fama da ita.

Daga karshe AMnesty ta ce "Mun nace gwamnati ta tabbatar da adalci a duk batutuwan da suka shafi duk wani dan Najeriya da suka hada da 'yan kungiyar IMN."

Takardar da ta haramta IMN

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement In Nigeria da na 'ta'addanci kuma haramtattu'.

Jaridar Punch Newspaper ce ta samu ganin wannan takardar inda ta ce ofishin ministan Shari'ar kasar ne ya nemi hukuncin.

Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu ba bu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane ba yin kira kansu da suna 'yan Shi'a."

Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya.

"Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungiyar a kundin gwamnati da kuma manyan jaridun Najeriya guda biyu." In ji takardar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda sun yi ta yin taho mu-gama da mabiya kungiyar IMN

Sifeton 'yan sanda ya ce IMN kungiyar ta'adda ce

Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce daga yanzu za su dauki duk wani dan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da aka fi sani da 'yan Shi'a a matsayin dan ta'adda bisa la'akari da hukuncin babbar kotu da gwamnati ta samu.

Sifeto Janar wanda ya bayyana hakan a hedikwatar 'yan sandan da ke Abuja a yayin wani taron manyan 'yan sanda na wata-wata ranar Talata, ya ce ayyukan kungiyar da yunkurin jefa Najeriya rikicin kabilanci.

Mohammed Adamu ya yi karin haske dangane da mambobin kungiyar IMN 63 da suka hada da mata bakwai wadanda ke hannun 'yan sandan, inda ya ce daga yanzu duk dan kungiyar ta IMN da suka kama to za su gurfanar da shi ne a gaban kotu domin fuskantar hukunci irin na ta'addanci.

Ya kara da cewa " ayyukan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da Sheikh Zakzaky ke jagoranta sun dade suna barazana ga tsaro da doka da oda na Najeirya da kuma zaman lafiya da jogaranci na gari da ma kimar tarayyar Najeriya na kasa mai cin gashin kai."

Sifeto Janar din ya kuma kawo wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar da ya ce sun yi karo da ayyukan kungiyar .

Ya ci gaba da cewa "saboda haka daga yanzu duk wani mutum da ya alakanta kansa da ayyukan kungiyar ta kowace hanya da za su iya tallafa wa IMN to dole a hukunta shi a matsayin dan ta'adda, makiyin kasa sannan kuma mai yi wa Najeriya zagon kasa.

"Ma'anar hakan ita ce duk wani nau'i na zanga-zanga da IMN take yi mun haramta kuma ya saba doka."

To sai dai sifeton na 'yan sanda ya yi karin haske cewa:

"A dai-dai lokacin da duk wani mabiyin mazhabar Shi'a yake da damar yin akidarsa ba tare da tsangwama ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su, kungiyar Elzakzaky ta Islamic Movement of Nigeria wadda ba ta yadda da kundin tsarin mulki ba da gwamnatin Najeriya, ita kadai ce kungiyar da aka haramta aka kuma bayyana ta da kungiyar 'yan ta'adda."

Labarai masu alaka