'Yan Shi'a sun yi amai sun lashe kan zanga-zanga

'Yan Shi'a a Najeriya Hakkin mallakar hoto NurPhoto
Image caption 'Yan Shi'a a Najeriya sun dade suna jimamin kame shugaban nasu da matarsa

Kungiyar 'yan Shi'a mabiya Sheik Ibrahim Elzakzaky ta IMN a Najeriya ta yi amai ta lashe inda a yanzu ta ce ta dakatar da zanga-zangar da take yi domin neman a sako shugaban nata, wanda ke tsare tun shekarar 2015.

A ranar Litinin ne mai magana da yawun kungiyar ya shaida wa BBC "babu gudu ba ja da baya" duk da umarnin da wata kotu ta bayar wanda ya haramta ayyukansu, yana mai cewa ba za su daina muzahara ba har sai an sako shugaban nasu.

Amma kwatsam sai ga shi ya fitar da sabuwar sanarwa yana ce sun dakatar da zanga-zangar, wacce suka shafe shekaru suna yi.

Ibrahim Musa ya ce "sun dauki wannan matakin ne da kyakkyawar niyya bisa girmama wasu manyan mutane da kungiyoyi a kasar wadanda suka tsoma bakinsu a zai kai ga warware rikicin da ke tattare da ci gaba da rike jagoranmu har shekaru hudu yanzu.

Sanarwar ta kara da cewa: "Idan har aka samu zanga-zanga a wasu wurare a fadin kasar, to hakan ya faru ne sakamakon rashin isar sakon a kan kari ko kuma ba a fahimci wannan sakon ba.

Ko kuma wasu jami'an tsaro ne suka shirya ta da manufar bata wa kungiyar suna kasancewar sun saba yin hakan ta yadda za a kalle mua matsayin 'yan ta'adda."

Kungiyar ta Islamic Movement ta kuma yaba wa kungiyoyin masu fafutuka na ciki da wajen gida wadanda suka yi gwauro da mari wajen ganin sun kare musu 'yancinsu da tsarin mulkin kasa ya ba su.

Daga karshe sanarwar ta ce "a shirye muke mu bi wasu hanyoyin wajen warware wannan batu da ya ki ci ya ki cinye wa. Muna kuma nanata bukakarmu ta neman a saki jagoranmu, Sheikh Ibrahim Elzakzaky da mai dakinsa da suke tsare tun 2015."

Takardar da ta haramta IMN

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement In Nigeria da na 'ta'addanci kuma haramtattu'.

Jaridar Punch Newspaper ce ta samu ganin wannan takardar inda ta ce ofishin ministan Shari'ar kasar ne ya nemi hukuncin.

Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu ba bu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane ba yin kira kansu da suna 'yan Shi'a."

Hakkin mallakar hoto SODIQ ADELAKUN
Image caption Magoya bayan Sheikh El-Zakzaky dai sun lashi takobin ganin an saki jagoransu

Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya.

"Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungiyar a kundin gwamnati da kuma manyan jaridun Najeriya guda biyu." In ji takardar.

Sifeton 'yan sanda ya ce IMN kungiyar ta'adda ce

Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce daga yanzu za su dauki duk wani dan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da aka fi sani da 'yan Shi'a a matsayin dan ta'adda bisa la'akari da hukuncin babbar kotu da gwamnati ta samu.

Sifeto Janar wanda ya bayyana hakan a hedikwatar 'yan sandan da ke Abuja a yayin wani taron manyan 'yan sanda na wata-wata ranar Talata, ya ce ayyukan kungiyar da yunkurin jefa Najeriya rikicin kabilanci.

Mohammed Adamu ya yi karin haske dangane da mambobin kungiyar IMN 63 da suka hada da mata bakwai wadanda ke hannun 'yan sandan, inda ya ce daga yanzu duk dan kungiyar ta IMN da suka kama to za su gurfanar da shi ne a gaban kotu domin fuskantar hukunci irin na ta'addanci.

Ya kara da cewa " ayyukan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da Sheikh Zakzaky ke jagoranta sun dade suna barazana ga tsaro da doka da oda na Najeirya da kuma zaman lafiya da jogaranci na gari da ma kimar tarayyar Najeriya na kasa mai cin gashin kai."

Sifeto Janar din ya kuma kawo wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar da ya ce sun yi karo da ayyukan kungiyar.

Ya ci gaba da cewa "saboda haka daga yanzu duk wani mutum da ya alakanta kansa da ayyukan kungiyar ta kowace hanya da za su iya tallafa wa IMN to dole a hukunta shi a matsayin dan ta'adda, makiyin kasa sannan kuma mai yi wa Najeriya zagon kasa.

Image caption A kan samu yanayin da kananan yara kan fita tituna domin tattakin neman saki jagoran IMN

"Ma'anar hakan ita ce duk wani nau'i na zanga-zanga da IMN take yi mun haramta kuma ya saba doka."

To sai dai sifeton na 'yan sanda ya yi karin haske cewa:

"A dai-dai lokacin da duk wani mabiyin mazhabar Shi'a yake da damar yin akidarsa ba tare da tsangwama ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su, kungiyar Elzakzaky wadda ba ta yadda da kundin tsarin mulki ba da gwamnatin Najeriya, ita kadai ce kungiyar da aka haramta."

Labarai masu alaka