Jagororin 'yan awaren Kamaru na yajin cin abinci

Sisiku Ayuk Tabe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jagoran masu neman ballewa daga Kamaru Sisiku Ayuk Tabe, wanda a yanzu yake fuskantar tuhuma kan cin amanar kasa

Jagororin yankin da ke neman ballewa daga kasar Kamaru wadanda ke tsare sun fara yajin cin abinci.

Sun bayyana cewa suna cikin damuwa kan lafiyar jami'ansu 200 bayan da aka gudanar da zanga-zanga a gidajen yari biyu cikin makon da ya gabata.

Wadanda aka tsaren sun ce suna fargabar cewa za a aiwatar da kisan kare dangi a kan mutanensu yankin da ke amfani da Turancin Inglishi.

Masu neman ballewar sun jima suna neman kafa kasar Ambazonia, wadda za ta hada yankunan da ke arewa maso gabashi da kuma Kudu maso Gabashin kasar.

Wato yankuna biyu da ake amfani da harshen Turancin Inglishi, a kasar da aka fi amfani da harshen Faransanci.

Lauyan kungiyar Joseph Fru ya bayyana wa shirin BBC na Focus on Africa cewa wadanda yake karewa suna fargabar yadda hukumomin Kamaru ke sanya ido kan 'yan Ambazonia, kuma a ganinsu hakan zai iya janyo a aiwatar da kisan kare dangi a kansu.

"Daya daga cikin ministocin Kamaru ya bukaci da a sanya ido kan dukkanin 'yan asalin kudancin Kamaru da ke zaune a yankin Kamaru inda ake amfani da harshen Faransanci," in ji shi.

BBC dai ba ta samu wata shedar da ta nuna cewa ana sanya ido kansu ba.

An kama shugabanin siyasar yankin Ambazonia ne a shekarar 2018 a Najeriya, daga baya aka mayar da su Kamaru inda suke fuskantar shari'a.

Masu amfani da harshen Ingilishi suna korafin cewa gwamnati da masu amfani da harshen Faransanci sun danne su.

Labarai masu alaka