Mutum '27,000' sun mutu sanadiyyar rikicin Boko Haram

Abuja Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum miliyan biyu ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 27,000 ne suka rasa rayukansu a tsawon shekara 10 na rikicin Boko Haram a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.

A farkon makon nan ne aka cika shekara 10 da kashe Shugaban kungiyar Boko Haram na farko Muhammad Yusuf.

Jami'in tsara ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Edward Kallon ne ya bayyana haka lokacin wani taro kan cika shekara 10 da fara rikicin, wanda aka yi a Abuja ranar Laraba.

"Rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar tsakanin shekarar 2009 zuwa 2019 ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 27,000," in ji Mista Kallon kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa. .

Kazalika, ya ce kimanin mutum miliyan biyu ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin.

Ya kuma ce Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba ta ji dadin yadda aka kashe da kuma sace ma'aikatan agaji ba.

Ya ce ma'aikatan sun mutu ne a bakin aiki, kuma "ba za mu taba mantawa da su ba."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Waiwaye kan ta'adin Boko Haram cikin shekara 10

A ranar 30 ga watan Yulin 2019 ne shugaban kungiyar Boko Haram na farko Mohammed Yusuf ke cika shekara 10 da mutuwa.

A kan haka ne BBC ta yi waiwaye kan takaitaccen tarihinsa a yayin da kungiyar ke ci gaba da kai hare-hare a Najeriya.

An haifi Ustaz Mohammed Yusuf ne kamar yadda aka fi sanin sa da shi a wancan lokacin, a watan Janairun 1970.

A shekarar 2002 ne ya kirkiri kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad, wacce aka fi sani da Boko Haram.

Mohammad Yusuf haifaffen kauyen Girgir ne da ke Jakusko a jihar Yobe, arewa maso gabashin Najeriya.

Yusuf ya yi karatun allo, daga baya kuma ya ci gaba da neman ilimi har ya rungumi ''akidar Salaf,'' wato fahimtar magabata tun daga kan sahabbai da wadanda suka biyo bayan su.

Ya sha fadar cewa yana bin akidar Salaf ce saboda koyi da fitaccen malamin Islaman nan Ibn Taymiyyah.

Sai dai malaman sunnah da dama a Najeriya sun musanta hakan.

Ya samu kwarin gwiwar bayyana akidarsa ne sakamon jin hudubobin na fitaccen malamin Islama na Masar Shukri Mustafa.

Ya yi imani da tabbatar da dokokin musulunci sau da kafa.

Muhammad ya yi ta gabatar da wa'azuzzuka a kan nuna haramcin karatun Boko, inda aka yi amannar ya samu dumbin mabiya, har wasu ma suka yi ta kona shaidar kammala karatunsu.

A wata hira da ya yi da BBC a 2009, Muhammad Yusuf ya ce bai yarda da batun nan na kimiyya da ke cewa duniya a zagaye take ba, yana mai cewa hakan ya sabawa Kur'ani da Hadisi.

Ya kuma ce bai yarda da batun silar asalin dan adam ba na Darwin da kuma cewa ''rana ce ke tsotse ruwan sama sai ya koma sama ya dawo, wannan ya sabawa ayoyin Ubangiji da suka yi magana akan hakan.''

Yusuf yana da mata hudu da 'ya'ya 12, kuma ana zaton cewa daga cikin su akwai Abu Musab al-Barnawi, wanda a tun 2016 yake ikirarin cewa shi ne magajin mahaifinsa, wato shugaban kungiyar Boko Haram ba Abubakar Shekau ba.

Rahotanni sun ce ya yi rayuwa irin ta jin dadi, inda yake amfani da manyan motoci kamar su Mercedes-Benz.

Bayan tashin hankalin da aka samu na 'yan kungiyar ta Boko Haram a 2009, sojojin Najeriya sun kama Muhammd Yusuf a gidan surukansa.

Daga bisani suka damka shi a hannun 'yan sanda. Daga baya 'yan sanda ne suka kashe shi a wajen hedikwatarsu da ke birnin Maidgurui.

Da fari dai 'yan sanda sun ce an harbe shi ne a yayin da yake kokarin guduwa, ko kuma ya samu raunuka ne a musayar wutar da aka yi da sojoji.

Wasu Labaran da za ku so ku karanta

Labarai masu alaka