Darusa 3 da Najeriya ta koya daga Boko Haram- Buhari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Darusa uku da Najeriya ta 'koya daga Boko Haram'

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana wasu darussa da ya ce gwamnnatin kasar ta koya daga kungiyar Boko Haram.

Ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da BBC yayin da aka cika shekara 10 da fara rikicin, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce fararen hula 27,000 ne suka mutu sanadiyyarsa.

Daya daga cikin darussan da ya lissafa shi ne cewa, ya kamata gwamnatoci su tashi tsaye wurin magance matsaloli tun suna kanana, "kafin karamar magana ta zama babba".

Sannan kuma ya ce maganar tsaro "ba ta gwamnati ba ce ita kadai, ta kowa da kowa ce".

Labarai masu alaka