Amurka za ta kara saka wa China haraji kan kayayyaki

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai kara saka haraji na kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin China da za su shiga Amurka na kusan dala billion 300.

Ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter bayan tattaunawar da Chinar ta yi da Amurkar ta gaza samar da wata nagartacciyar mafita.

Ana sa ran cewa wannan harajin zai fara aiki ne a watan Satumba kuma zai shafi dukkanin kayayyakin da za su shiga Amurka daga China.

A jerin sakonnin da Mista Trump ya aika a shafinsa na Twitter, ya fara ne da jinjinawa sabuwar tattaunawar yarjejeniyar da kasashen biyu suka yi.

Ya bayyana tattaunawar da aka yi a wannan makon a Shanghai a matsayin tattaunawa mai kyau kuma mai amfani kafin daga baya ya bullo da wannan sabuwar barazanar ta shi ta kara zabga haraji.

Da alamu Mista Trump ya fusata kan yadda Chinar ta gaza samar da kayayyakin da ya kamata ta samar kamar yadda tayi alkawari.

A lokacin da Mista Trump ke daf da shiga jirgin sama ya shaida wa manema labarai cewa yana da ikon saka haraji ko zaftarewa domin matsa wa China lamba ko hura mata wuta.

Mista Trump din ya ce ''Shugaba Xi mutum ne wanda nake so, ina ganin yana da ra'ayin wannan yarjejeniya, amma maganar gaskiya ita ce ba shi da azarbabi.

''Ya taba cewa kasarsa za ta rinka sayan kayayyaki daga manomanmu kuma bai yi hakan ba. Ya kuma ce zai yi kokarin hana shigar da kwayar Fentanyl Amurka, duk daga China ake shigo da ita amma ya gaza.''

Dubban 'yan Amurka ne ke mutuwa saboda Fentanyl, in ji Mista Trump.

Ya ce ''Kuma muhimmin abu shi ne ko wacce shekara China na samun biliyoyin daloli duk shekara tana kara gina kanta, mu ma lokaci ya yi da za mu kara gina kasarmu.''

Wannan harajin dai ba zai fara aiki ba sai watan Satumba wanda hakan zai ba Chinar damar yin gyararraki ko watakila Trump ya janye harajin kafin a fara wata sabuwar tattaunawar a Washington.

A shekarar da ta gabata ne Mista Trump ya zabga haraji kan kayayyakin China na kusan dala biliyan 250, amma a wannan karon harajin zai yi tasiri matuka ga Amurkawan da za su saya kayayyakin sakamakon tsada.

Wannan harajin zai shafi komai tun daga kayayyakin wasan yara har zuwa wayoyin sadarwa haka zalika farashin na'urar kwamfuta ma zai yi karuwa.

Labarai masu alaka