Ranar Lahadi za a yi Babbar Sallah a Najeriya – Kwamitin Ganin Wata

Sallah Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ranar Lahadi 11 ga watan Agusta ne za a yi bikin Babbar Sallah a Najeriya, kamar yadda Sakataren Kwamitin Ganin Wata a Najeriya Malam Yahaya Boyi ya shaida wa BBC.

Sai dai bai yi karin haske ba game da tabbacin ganin jinjirin watan Dhul Hijjah a kasar, ko kuma ya dogara ne da ganin watan Saudiyya.

Kodayake kwamitin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ranar Juma'a ce 1 ga watan Dhul Hijjah, 1440 BH.

Kazalika, kwamitin ya wallafa wani sako da ke cewa ba a samu labarin ganin jinjirin watan a fadin Najeriya ba a ranar Alhamis.

"Bayan tuntubar malamai an ayyana ranar 2 ga watan Agusta 2019 a matsayin 1 ga watan Dhul Hiijjah, 1440 bisa dogaro da ganin watan Saudiyya," in ji sanarwar.

Tun da farko kasar Saudiyya ta bayyana cewa bayan ganin jinjirin watan a fadin kasar a ranar Alhamis, za a yi hawan Arfa ne a ranar Asabar wato 10 ga watan Agusta, kuma washegari a fara bukukuwan Sallar Layya a fadin kasar.

Kimanin Musulmi miliyan biyu ne za su yi aikin hajji a bana.

Aikin hajji dai na daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci biyar, da kowace shekara miliyoyin Musulmi daga sassa daban-daban kan hallara a kasar Saudiyya domin aiwatarwa.

Labarai masu alaka