A yi wa Zakzaky adalci – Sheikh Bala Lau

Shugaban Kungiyar Izala a Najeriya Shiakh Bala Lau

Asalin hoton, Jibwis Nigeria

Bayanan hoto,

Shaikh Bala Lau ya ce ba ya jin dadin yadda wasu suke kokarin siyasantar da batun 'yan Shi'a

Shugaban Kungiyar Izala ta JIBWIS a Najeriya Shaikh Abdullahi Bala Lau ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi wa jagoran 'yan Shi'a Shaikh Ibrahim Zakzaky adalci.

Malamin addinin ya bayyana hakan ne lokacin da yake hudubarsa ta Juma'a a masallacin hedikwatar kungiyar ta JIBWIS da ke Utaku a Abuja ranar Juma'a.

Ba wannan ne karon farko ba da wani babban malamin sunnah a kasar yake magana kan batun jagoran 'yan Shi'a a kasar ba.

Shaikh Ahmad Gumi ya taba kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sake shi a baya.

Shaikh Bala Lau ya ce: "Babu wanda ba ya son a yi wa shugabansu (Zakzaky) adalci. Ko kafiri ne a yi wa adalci. Idan abin da ya yi ba daidai ba ne a hukunta shi saboda gani ga wane, ya isa wane tsoron Allah."

Ya ci gaba da cewa: "Idan ba a yi masa hukunci ba zanga-zanga da tawaye za su sa a sake shi. Idan kuwa aka sake shi to ranar da duk aka kama wani shugaba na kowane addini mabiyansa su ma su fito su yi zanga-zanga, su yi abin da suka ga dama domin a saki shugabansu.

"Daga nan babu sauran zaman lafiya kenan," in ji shi.

Kazalika, ya ce "idan jagoran 'yan Shi'an bai yi laifi ba, to a sake shi. Idan ko ya yi laifi a yi masa hukunci kamar yadda ake yi wa kowane dan kasa mai laifi. "Idan aka yi haka an zauna lafiya."

Shaikh Bala Lau ya kuma kara da cewa ba ya jin dadin yadda wasu suke kokarin siyasantar da batun.

Ya ce: "Akwai wasu da suke kokarin yin amfani da matsalar wajen hada 'yan Izala fada da 'yan Darika a Najeriya. Suna cewa idan aka gama da 'yan Shi'a su za a koma wa."

Malamin ya ce babu gaskiya a cikin wannan ikirarin, kuma ma ya ce Izala ta yi tarayya da darika a wasu bangaorin addini, kamar girmama sahabbai baki daya.

Ya kara da cewa 'yan darika sun fi kusa da 'yan Izala fiye da kusancin su da 'yan shi'a.

A gefe guda kuma, shugaban kungiyar ya soki yadda BBC ta yi kuskuren danganta Muhammad Yusuf tsohon shugaban Boko Haram da jami'ar Musulunci ta Madina a wani rahoto da ta wallafa ranar Talata.

Labarin an wallafa shi ne saboda cika shekara 10 da aka yi da fara rikicin Boko Haram a Najeriya.

Sheikh Bala Lau ya yi kira ga BBC din da ta gaggauta gyara kuskuren da ta yi.

Sai dai tuni BBC ta gyara wannan kuskure 'yan sa'o'i bayan wallafa labarin kuma ta nemi gafara.