Hajj 2019: Musulman duniya sun fara ayyukan ibada

Mina birnin Tantuna
Image caption Alhazai suna fara yada zango ne a Mina kafin su tafi zuwa Arafa, su koma Muzdalifa, su je Makka domin yin jifa, sannan su koma Mina.

Kimanin Musulmi miliyan biyu da rabi ne suka fita birnin Mina tantuna domin fara aikin hajjin bana.

Aikin ibadar na shekara-shekara yana farawa ne ranar takwas ga watan Zul-hajji, yayin da maza ke cire kayan gida su daura harami, sannan su fara ibadar. Mata suna ibadar ne da kayan su na yau da kullum.

Tuni dai Musulman suka wuni a filin na Mina, sannnan a gobe Juma'a za su tafi Arafa domin wuni a can. Arfa dai ita ce rukuni mafi girma a aikin hajji.

Alhazai suna fara yada zango ne a Mina kafin su tafi zuwa Arafa, su koma Muzdalifa, su je Maka domin yin jifa, sannan su koma Mina.

Aikin hajji na daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.

A duk shekara Musulmi daga fadin duniya na tafiya Maka a kasar Saudi Arabiya domin gudanar da aikin ibadar.

Najeriya na daga kasashen da alhazansu da dama ke halartar aikin hajjin. Hukumar aikin hajji ta kasar NAHCON ta ce mutum 45,000 ne suka halarci aikin hajjin na bana.

NAHCON ta ce ta yi tanade-tanade da sauye-sauye da dama domin saukaka wa 'yan Najeriya aikin na bana.

Image caption Alhazai suna yin kwana biyu ko uku a Mina

Labarai masu alaka